Matashi Mai Shekara 24 Ana Zargin Sa Da Kashe Mahaifinsa A Bauchi
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Ƙaddamar da Hasken Solar a Dajin Yankari
Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wani matashi Mai Shekara 24 bisa zargin kashe mahaifinsa ta hanyar yin amfani da sanda yadda ya bugi mahaifin a kansa kuma rai yai halinsa, wanda hakan ya yi sanadiyar faɗuwar dattijon nan take ya mutu.
Lamarin ya faru ne a garin Uzum dake ƙaramar hukumar Giaɗe a jihar Bauchi inda yanzu haka ’Yan sanda suka kama matashin mai shekara 24 kan zargin ya kashe mahaifin nasa mai shekaru 70.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar Yan sanda CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce matashin ya yi amfani da sanda ne ya bugi mahaifin nasa a ka, nan take dattijon ya faɗi ya mutu.
Wani mazaunin ƙauyen Uzum da ke Giaɗe ya ce ana zargin ya lakaɗa wa mahaifinsa duka ne da sanda yayin da suke taƙaddama a gida da misalin karfe 10:30 na daren ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
A karanta:Tsohon ma’aikacin gidan rediyo Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu
Ya ce, “Ba mu san abin da ya faru ba, amma dai mun ji wata babbar hayaniya tsakaninsu, lamarin da ya sa shi ya bugi mahaifin nasa da sanda a ka, mahaifin ya faɗi a sume.
“Mun sanar da ’yan sanda suka zo suka kai shi babban Asibitin da ke Giaɗe, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa a asibitin.”
Ahmed Wakili ya bayyana wa manema labarai a ranar Juma’a a Bauchi cewa, “Da samun labarin kwamishinan ’yan sandan jihar Sani Omolori ya umurci jami’in ’yan sanda (DPO) da ke kula da Ofishin Shiyyar Giaɗe da ya gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru. Don haka jami’an ’yan sanda sun je wurin da lamarin ya faru inda suka sami marigayin a kwance jina-jina, suka kai shi babban Asibitin Giaɗe kuma likita ya tabbatar da rasuwarsa. An kuma miƙa gawarsa ga iyalansa domin yin jana’izarsa kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada.”
Read also: Rikicin Manoma da Makiyaya Yai Sanadiyar Rasa Rayukan Ƴansanda 5 da Ɗanagaji A Bauchi
A karanta:Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano
Yace rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike, wanda ake zargin kuma yana hannun su kuma bayan an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.



























