Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Daga Sunusi K/Na’isa
Shugaban Hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji ya bayyana hakan a lokacin da suka kai ziyara ofishin Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori domin kulla alakar aiki haɗi da taimakawa juna ta bangaren inganta tsaro a jihar.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Sheikh Daneji ya bayyana cewar sun kawo ziyarar ne domin haɗa hannu wajen faɗakar da matasa tare kuma da taimakawa rundunar Yansanda a bangarori da dama.
Ambaliya ruwa ta hallaka mutane sama da 100 a jihar Texas ta Amurka
A jawabinsa Kwamishinan Yan Sanda CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana jin daɗinsa bisa wannan ziyara, tare da bada tabbacin bayar da gudummawa ga Hukumar Shari’ar a dukkanin bangarorin da suke da hurumi akai, musamman bangaren yakar ɗabi’ar Fadace-fadacen daba da kwacen waya da ta addabi jihar a kwanakin nan.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Buƙatar Su
A yayin ziyarar Sheikh Abbas Daneji yana tare da Kwamishina na ɗaya Gwani Hadi da na biyu Sheikh Ali Danabba da sauran Mambobi da Daraktocin hukumar.




























