Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano

Abba Al Mustapha
Abba Al Mustapha

Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano

Daga Sunusi K/Naisa

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta ce ba ta soke ko haramta sana’ar downloading a faɗin jiha ba, duk da rahotannin da ke yawo cewa an dakatar da sana’ar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, a ranar Alhamis 16-07-2026.

Sanarwar ta ce babu wata hukuma da ta tuntuɓi hukumar tace Fina-finai da dab’i kafin ɗaukar irin wannan mataki, duk da cewa masu sana’ar downloading na daga cikin waɗanda hukumar ke da alhakin sa ido kan ayyukansu bisa tanadin dokar da ta kafa ta.

Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai

Haka kuma Hukumar ta ce tuni ta fara bincike kan wani saƙon murya da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin wasu masu sana’ar da yaɗa bidiyoyin tsiraici ko. Sai dai ta ce binciken farko ya nuna cewa ana zargin muryar da ke cikin saƙon ba daga Jihar Kano take ba, yayin da bincike ke ci gaba.

A cewar sanarwar, hukumar ta tura jami’anta a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin gano masu yaɗa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya, tare da ɗaukar matakin doka a kansu idan aka same su da aikata laifi.

Hukumar ta kuma ce ta yi la’akari da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin masu sana’ar downloading da masana’antar Kannywood, tare da muhimmancin samar wa matasa hanyoyin samun abin dogaro da kai. Saboda haka, ta jaddada cewa ba ta haramta sana’ar ba, sai dai za ta ci gaba da hukunta duk wanda aka kama yana amfani da ita wajen yaɗa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci.

Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi, Mutane na Sambarka

A ƙarshe, hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta buƙaci jama’a su ci gaba da ba ta haɗin kai tare da kai mata sahihan bayanai domin tabbatar da bin doka da oda a jihar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...