Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: Auren Gata Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne, Inji Sheik Hadi MaiHula
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗa Sheikh Bazzallah Nasiru Kabara a matsayin sabon shugaban Hukumar Tace fina-finai ta jihar Kano.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Farouk Ibrahim ya sanar da hakan a ranar Laraba tare da miƙa takardar naɗin a hukumance.
A wani saƙo da Sakataren Yaɗa Labarai ga Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Musa Tanko Muhammad, ya fitar, ta ce naɗin Sheikh Bazallah Kabara ya fara aiki nan take.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yanke shawarar amincewa da naɗin ne bayan la’akari da gogewa, kwarewa da tarihin Sheikh Kabara, wanda gwamnati ke ganin zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa da tsare harkar fina-finai da ayyukan kirkira a jihar.
Gwamnatin Jihar Kano ta yaya sabon shugaban murna tare da neman jagorancin Allah, gwamnatin ta nuna ƙwarin gwiwar cewa sabon shugaban hukumar zai jagoranci ayyukan tacewa, tsari da daidaita harkokin fina-finai bisa al’adu, ɗabi’u da ƙa’idojin jihar, tare da gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa da jajircewa



























