Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Daga Sunusi K/Na’isa
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan mutuwar ɗalibai biyu a makarantar sakandiren kwana ta gwamnati da ke Bichi sakamakon Gwale-Gwale.
Waɗanda aka kashen, sune Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa, an yi zargin wasu ɗaliban ne suka kai musu hari ta hanyar amfani da wasu karafa tare da basu “Gwale-Gwale”.
A cewar rahotannin farko, an kai wa ɗaliban wannan muna harin ne a matsayin wani nau’i na ukuba da aka ce manyan daliban suka aiwatar akan ɗaliban bisa zarginsu da aikata wani laifi. A inda hare-haren ya yi sanadin jikkatar mutane, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsu.
Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan ilimi na jihar Kano, Dakta Ali Haruna Makoda, ta bakin babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike na gaskiya. Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa duk wadanda aka samu da laifi za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
“Ba za mu amince da duk wani nau’i na rashin bin doka da oda a cikin makarantunmu ba. Rayuwa da lafiyar ɗalibanmu su ne babban fifikonmu,” in ji Sakatare yayin ziyarar da ya kai makarantar.
Ya kuma gargadi ɗalibai da su guji ɗaukar doka a hannunsu, inda ya bukace su da su rika kai rahoton korafe-korafe ko damuwa ga hukumomin makarantar da suka dace.
Da yake jawabi, Daraktan Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Abbas Abdullahi, ya yi Allah wadai da lamarin da kakkausar murya. Ya jaddada bukatar ladabtarwa sannan ya bukaci ɗaliban da su rinka kiyaye doka.
‘Yan uwan waɗanda abin ya shafa sun bayyana alhininsu tare da yin kira ga gwamnati da ta tabbatar an yi adalci. Malam Ibrahim Yusuf Dungurawa, ɗan uwa ne ga ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, ya roƙi a gaggauta gudanar da bincike na gaskiya.
Malam Idris Garba Tofawa, mahaifin ɗalibi na biyu da ya rasu, ya bayyana cewa, “Mun amince da faruwar lamarin a matsayin ikon Allah, amma muna roƙon hukumomi da su ɗauki kwakkwaran mataki domin kada irin wannan lamari ya sake faruwa.
Read also: Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA
Daraktan wayar da kan jama’a a ma’aikatar ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru, ya jaddada aniyar gwamnati na bankado gaskiyar lamarin tare da hukunta duk masu laifin.
Ambaliya ruwa ta hallaka mutane sama da 100 a jihar Texas ta Amurka
A halin yanzu kuma tuni hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta bayar da sanarwar ɗalibai goma sha ɗaya (11) da ake zargin da hallaka ‘yan uwansu, sun shiga hannu.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Abdullahi Kiyawa ya sanar da haka ga jaridar Punch. Ya kuma bada tabbacin hukumar na gudanar da bincike kamar yadda doka ta shimfida gami da alƙawarin gurfanar da waɗanda ake zargin ga gaban kotu, domin girbar abin da suka shuka.



























