Gwamnatin Kano ta nemi jami’an tsaro su Kama tsohon Gwamna Ganduje da Barau bisa zargin kalaman tunziri
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Ka Daina Siyasartar Da Harakar Tsaro, Barau Jibrin Ya Gargaɗi Gwamna Kano
Majalisar zartarwa jihar Kano ta ce kalaman tsohon gwamnan Ganduje na kafa Hisba da jawabin Mataimakin shugaban Majalisar Tarayya Barau Jibril su suka haifar da rashin tsaro a Kano.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya shaida hakan a taron manema labarai kan zaman majalisar zartaswar jihar karo na 34.
Kwamishina ya ce Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin mulkin Alhaji Abba Yusuf tayi Allah Wadai da kalaman tsohon gwamnan jihar Dr.Abdullahi Umar Ganduje da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibiril akan tsaron Kano wanda hakan ya janyo aka kawo hare hare wasu kananan hukumomin jihar.
Tsohon Gwamna Jigawa Sule Lamido Ya ce Zasu Samawa Jam’iyyar PDP Mafita Kwanana
Kwamishinan Wayya ya ce zaman majalisar zartarwar ya amince da bukatar kama Ganduje da Barau domin tuhumarsu kan zargin hana Kano zama lafiya.
Inda ya ce ” Kasancewarsu shugabanni maimakon su taimakawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cimma nasara na yaƙi da yan ta’adda, amma sun zauna suna karawa tunzura lamari wanda ka iya kawo barazana ga jihar Kano wacce ita ce mafi zaman lafiya a Najeriya”.
Kwamishina ya kuma ce Gwamna Abdullahi Ganduje a shekara 8 da yayi yana mulki wacce gudunmawa ya bawa hukumar Hisba, banda koma baya da ta samu balle har ya kafa wai Hisba a Kano, in ji Kwamishina Waiya.
Idan za a tuna, kwanan nan ne Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi ikararin kafa sabuwar hukumar Hisba mai zaman kanta ta Jihar karkashin kulawarsa abinda gwamnatin Kano tace ya saba doka Kuma takalar rigima ne da tada fitina.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Bayan ikirarin kafa Hisba mai zaman kanta, Gwamnatin Kano ta kuma zargi Ganduje da wasu kalaman tunzuri akan sha’anin tsaro wanda ya sabawa Doka.
Haka Kuma gwannatin ta zargi Sanata Barau Jibiril da tunzura jama’ar Kano saboda kalaman da yayi na cewa Kano ta koma baya abinda shima ya janyo Cece-Kuce.
Idan za a tuna,a kwanan nan ne Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi ikararin kafa sabuwar hukumar Hisba mai zaman kanta ta Jihar ƙarƙashin kulawarsa abinda gwamnatin Kano tace ya saɓa doka Kuma tsokanar rigima ne da kuma tayar da fitina a jihar.
Haka zalika gwannatin Kanon ta zargi Mataimakin shugaban Majalisar Tarayya Sanata Barau Jibiril da tunzura jama’ar saboda kalaman da yayi na cewa Kano ta koma baya abinda shima ya janyo gutsiri tsoma.
Don haka Gwamnatin ta ce baza ta zuba ido ta bar wasu na kalaman da basu dace ba, bisa haka ta nemi hukumomin tsaro da su tabbatar sun kama Ganduje da Barau domin tuhumarsu.
Babbar Kotun Tarayya Abuja ta yanke hukunci ga wanda ya kitsa munanan hare-hare a Kano
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha
Gwamnatin Kano ta kuma shawarci jama’a da su rika tabbatar da sahihancin labarai kafin yadawa, domin kaucewa tayar da hankulan jama’a bisa labaran da ba su da tushe.
Kimanin sana da Naira Biliyan 54 Majalisar Zartaswar ta amince a Kashe domin aiwatar da ayyukan raya kasa a sassa daban-daban a jihar ta kano.



























