Connect with us

Hi, what are you looking for?

Siyasa

Ka Daina Siyasartar Da Harakar Tsaro, Barau Jibrin Ya Gargaɗi Gwamna Kano

DSP Barau Jibrin
DSP Barau Jibrin

Ka Daina Siyasartar Da Harakar Tsaro, Barau Jibrin Ya Gargaɗi Gwamna Kano

Daga Sunusi K/Naisa

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin, ya gargaɗi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya daina ƙoƙarin siyasantar da batun tsaro, ya mayar da hankali wajen warware matsalolin da Kano take ciki.

Sanata Barau ya ƙaryata zargin gwamnatin jihar cewa ya yi wasu kalamai da za su iya kawo tangarɗa ga tsaron jihar, yana mai ƙalubalantar gwamnati da ta nuna hujjar da take da ita akan iƙirarin hakan.

Ya ce matsalar tsaro ba ta buƙatar rikici tsakanin ɓangarori, sai ma a nemi haɗin kan masu ruwa da tsaki domin magance ƙalubale matsalar tsaron da ke faruwa a wasu sassan Kano.

Gwamnatin Kano ta Nemi Jami’an Tsaro Su Kama tsohon Gwamna Ganduje da Barau Bisa Zargin Kalaman Tunziri

Sanatan ya kuma zargi gwamnatin jiha da rashin gudanar da mulki yadda ya kamata, yana mai cewa hakan ya janyo koma bayan ga Kano Sosai .

Ya bayyana wasu daga cikin gudummawar da ya ce ya bayar domin inganta tsaro, ciki har da ba da motocin sintiri, babura, gyaran ofisoshin ‘yan sanda da gina sabbin cibiyoyin horar da jami’an tsaro.

Sanarwar hakan ta fito daga hannun mai taimakawa mataimakin shugaban majalisar dattawan kan harkokin yaɗa labarai Isma’il Muddasir ya fitar.

Rungumar Tsarin Majalisar Wuccin Gadi A Najeriya Na Iya Ajiye Biliyoyin Naira A Shekara, In Ji Ali Ndume

Sanarwar ta ce maimakon gwamnatin Kano ta zarge shi, ya kamata ta yi koyi da ayyukan da yake yi domin tsare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...