Ko Kasan Sabbin Kwamishinonin Da Gwamna Kano Abba Yusuf Ya Naɗa?
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗa Sabbin Kwamishinoni tare da rantsar dasu a yau Litinin.
Kwamishinonin sune kamar haka:
1. Alhaji Shehu Wada Sagagi, wanda zai kula da ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta kano
2.Kwamared Ibrahim Abdullahi Waya, Kwamishina Ma’aikatar yaɗa Labarai ta jiha.
3. Dr. Dahir Muhammad Hashim an amince ya rike ma’aikatar kula da Muhalli da Chanjin Yanayi.
Ka Iya Karanta Wanna:Daukewar Wutar Lantarki ta ‘Yan Dakikoki ta Jawo Biyan Diyar Sama Da Naira Miliyan 375
Read also: Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa
4. Alhaji Abdulkadir Abdussalam, an nada shi a matsayin Kwamishina gwamna Ma’aikatar kula da Raya karkara ta Kano
5. Dr. Isma’ila Aliyu Dan Maraya , zai kula da Ma’aikatar Kudi ta Kano.
6. Dr.Gaddafi Sani Yakubu , an turashi Ma’aikatar Kula da makamashi ta Kano
7. Dr.Nura Iro Ma’aji , Ma’aikatar Kula da yadda ake bada kwangiloli da bibiyar ayyukan gwamnati
8. Adamu Aliyu Kibiya Daga an sauya masa ma’aikata daga kwamishinan Kasuwanci zuwa Ma’aikatar Jin Kai.
Read also: One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano
Ka Iya Karanta Wanna:Horon Tukin Mota: Shugaban Karamar Hukumar fagge Salisu Masu Yayi Kira Ga Matasa Su Amfani Damar
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce ya dauki matakin samar da sabbin kwamishinonin ne domin inganta ayyukan gwamnati da Kuma kawo cigaba a Kano.



























