Rungumar Tsarin Majalisar Wuccin Gadi A Najeriya Na Iya Ajiye Biliyoyin Naira A Shekara, In Ji Ali Ndume
Daga Abdu Ado K/Naisa
Read also: BASHI NA DAF DA DURKUSAR DA NAJERIYA
Sanatan Borno ta Kudu, Muhammed Ali Ndume, ya ce Najeriya na iya ajiye maƙudan kuɗaɗe na naira a duk shekara idan aka rungumi tsarin majalisa ta wucin gadi.
Yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, Ndume ya ce kuɗin da ake kashewa wajen kula da Majalisar Dokoki a tsarin zama ko da yaushe ba zai ɗore ba, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke fama da matsalolin kuɗi da tsaro.
Kuɗin gudanar da gwamnati ya yi yawa sosai. Idan ’yan majalisa suka zauna na wucin gadi, gwamnati za ta ajiye biliyoyi,” in ji shi.
Ya ce za a iya sauya akalar kuɗin zuwa bangaren tsaro da sauran muhimman abubuwan ƙasa.
Read also: Majalisar Dokokin Kano ta goyi bayan Gwamna Yusuf Ya fita Daga Jam’iyyar NNPP
Ndume ya danganta tsadar gudanar da gwamnati da manyan ƙalubale da ke hana ƙasar yin nasara wajen yaƙi da rashin tsaro.
Ya ce Najeriya ba za ta iya jure ɓarnar kashe kuɗi ba a yayin da ake fuskantar ta’addanci a Arewa maso Gabas da ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da masu garkuwa da mutane da kuma ƙaruwar laifuka daban-daban.
A wani ɓangaren na fafutukar rage kashe kuɗi, sanatan ya soki ci gaba da kasancewar ’yan sanda da ke tare da sanataci da sauran manyan mutane duk da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye jami’an tsaro daga irin wannan aiki.
Idan za a tuna Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Sufeto Janar na ’Yan Sanda Najeriya, Kayode Egbetokun, da ya janye jami’an daga aikin kare manyan mutane ya kuma tura su zuwa fagen yaƙi da ta’addanci da samar da tsaro.
“Amma har yanzu, ’yan siyasa na tare da ’yan sanda,” in ji Ndume, yana kira ga Babban Sufeton da ya tabbatar da cikakken bin umarnin na shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa tura ’yan sanda daga aikin kare manyan mutane zuwa aikin al’umma da na fagen yaƙi zai ƙara inganta tsaron ƙasa fiye da barin su ga mutum ɗaya.
Read also: Murtala Garo Zai Bayyana A Majalisar Dokokin Kano Don Tantancewa
Tsohon Gwamna Jigawa Sule Lamido Ya ce Zasu Samawa Jam’iyyar PDP Mafita Kwanana
Ndume ya ce tsarin tsaron ƙasa ya yi ƙunci kuma yana bukatar “haɗa hannaye wajen yin aiki,” yana mai jaddada cewa dubban jami’an suna maƙale wajen rakiyar ’yan siyasa da masu tasiri waɗanda za su iya rayuwa ba tare da irin wannan rakiyar ba.



























