Tsohon Gwamna Jigawa Sule Lamido Ya ce Zasu Samawa Jam’iyyar PDP Mafita Kwanana
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Tsohon Gwamna jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido Ya ce dole zasu samawa jam’iyyar PDP da mutanan ta mafita nan bada dadewa ba.
Alhaji Sule Lamido Ya furta haka da yake karɓar Kungiyar tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi na jam’iyyar PDP na jihar Jigawa (Forum of Former PDP Local government council, Jigawa State) a ranar Alhamis da suka kai ziyara a ofishin da.
Sule ya fara da bada tarihin siyasar sa tun daga PRP, SDP har zuwa PDP, kuma ya tabbatar da cewa baya neman komai a PDP sai adalci a matsayinsa na ɗan ƙasa kuma ɗan jam’iyya. Ya ƙara da cewa ” Babban abun da yake masa ciwo shine ace an wayi gari ana faɗan shugabanci a jam’iyyar PDP a inda yake ganin hakan abun kunya ne a gare su” inji tsohon Gwamna.
Ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP yayi Minista a cikinta kuma yayi gwamna da sauran manyan muƙamai don haka jam’iyyar ke binsa bashi, ba wai shi yake bin jam’iyyar PDP bashi ba.
Read also: Duk Wanda Ya Tafi Jam’iyyar APC ya Tafi Shi Kaɗai, In ji Sanata Rufai Sani Hanga
Ɗan takarar shugabancin jam’iyyar PDP a ƙasa, ya ce yaje kotu ne don nemawa kansa haƙki ba wai don matsalar samun muƙami da ake ta rade radi ba. Kuma babban matsalar baya son a shiga zabe babu tsayayyyen shugabanci, wanda hakan zai iya sanyawa a kwace mulki kamar yadda ta faru a lokutan baya musamman a jihar Zamfara, wanda gwamnoni irinsu Osun da Taraba da Zamfara ɗin ke nuna rashin sanin makomarsu idan an tafi akan haka a jam’iyyar ta PDP.
Yayi Kira da gwamnoni irinsu Fintiri na Adamawa da Bala Kaura na Bauchi da manyan jigajigan jam’iyyar kamar su Saraki da kowa ya ajiye son zuciyarsa ayi afuwa ga Juna a tunkari matsalar da jam’iyyar ke ciki da kuma makomar Najeriya.
Game da Matsayar sa kuwa yace ” A Ƙara haƙuri zuwa 9 ga Disamba”, A ƙarshe ya bada tabbacin samun nasara da sanin matsaya game da makomar jam’iyya da ‘ya’yenta nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Da suke miƙa bayanin bayan taron da suka rubuta wanda suka zauna a ranar 18 ga watan Nuwamba shugabannin tsofaffin Ƙungiyar ƙananan hukumomi sun buƙaci tsohon Gwamna Sule Lamido da ya bayyana musu matsayarsa a Jam’iyyar PDP a matsayinsa na jagoran tafiyar su domin sanun alkibula.
Takardar bayan taron da mutane 17 suka sanya wa hannu sun ce bukatar ta biyo bayan biyo matsalar shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a ƙasa. Kuma sunyi ala’wadai da shugabancin na ƙasa sabo da yadda suka ci zarafin jagoran na su, Alhaji Sule Lamido na hanshi tsaiwar takarar shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.
Read also: Kotin ƙoli: Nura Husaini Ya Bayyana Nasarar Gwamna Abba A Matsyin Nasara Ga Al’ummar Kano
Nambobin Wayar Kar-Ta-Kwana Daga Hukumar Yan Sandan Jihar Kano
Jawabin bayan taron yace babu wanda yafi jagoran su chanchanta ya tsaya takara fiye da shi, duba da kasancewar sa ɗaya daga cikin waɗanda suka yanke wa jam’iyyar cibiya tun daga matakin G9 da G18 wanda kuma bai taɓa rawa ba.
Sun bada tabbacin ci gaba da bashi goyan baya a dukkanin inda ya sanya gaba.



























