Duk Wanda Ya Tafi Jam’iyyar APC ya Tafi Shi Kaɗai, In ji Sanata Rufai Sani Hanga
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Tsohon Gwamna Jigawa Sule Lamido Ya ce Zasu Samawa Jam’iyyar PDP Mafita Kwanana
Sanatan Kano ta tsakiya Alhaji Rufai Sani Hanga ya ce duk wanda ya tafi jam’iyyar APC a wanna lokaci ya tafi shi kaɗai.
Hon. Rurai Hanga ya bayyana hakan a wata hira da akai da shi a kafar yaɗa labarai ‘Jarida Arewa’, wacce ta sanya hirar fefan bidiyo a kafaffan sada zumunta.
Tsohon ɗan jam’iyyar APC, kuma Sanata a tutar NNPP a yanzu ya ce bazai kafara ba duk zaɓaɓɓen da ya tafi wata jam’iyya a yanzu yai wa kansa. In da yace su waɗanda ke takara a waɗancan jam’iyyar ya’ya za ai dasu?
Sanatan ya yi wannan jawabi bisa raɗe-raɗin Gwamna Kano Abba zai koma jam’iyya mai mulki a Najeriya ta APC, in da ya ce wannan labarin ƙarya ce kawai, kuma abin da ba zai yiwu ba ne. ” Ko da yake ni banji daga bakin Abba ba, amma ba zan ce wani abu ba”. In ji Hangan.
Read also: Jam’iyyar NNPP ta Kori Shugabanta Na Kano, Hashimu Dungurawa daga Jam’iyya
Ƙungiyar RATTAWU Na Ta’aziyya Ga Gwamna Abba Yusuf Bisa Rashin Hazziƙan ‘Yan Majalisa Ungogo da KMC
“Idan ko haka ne duk mutumin da ya ce Abba ya koma APC bai tunani ba kuma ba masoyin sa ba ne, kuma ya kamata Gwamna Abba yai masa hukunci”.
Da aka tambaye shi ba ya ganin da sanin tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, Abba zai koma APC wanda daga bisani shima Kwankwason zai bi shi, sai ya ce ” Wannan wasan Kwaikwayo ke nan , toh! Mai zai hana jagoran ba zai yi gaba ba ko kuma ya jagoranci tafiyar? Wanna babu basira a wanna zancen in ji Sanata Rufai Hanga.
Ya ce jam’iyyar da ta cire tallafin man fetur ga shi kuma suna ƙoƙarin ƙaƙabawa talakawa sabon haraji duk da tsanin rayuwar da ake ciki, wanda talaka sai ya yi kuka da idanunsa, kuma a ce Abba zai koma can, ya ce baya jin wannan maganar haka take.
Domin mu kanawa ba a cin ammana muyi wa mutum tafi, kuma muna tausayi ga wanda akai wa butulci domin muna da kunya, in ji Hanga.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
NIN Yanzu Zai Aiki a Matsayin TIN ga Mutane, Hukumar Haraji ta Tarayya Ta Sanar da Hakan
Don haka Sanata Rufai Hanga, ya ce yana jam’iyyar NNPP kuma yana jaddada goyon bayansa ga Jagora Rabi’u Musa Kwankwaso dubu bisa dubu, saboda hanyar sa itace hanyar talakawa wacce babu kuskunda a cikin ta.




























