Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

NIN Yanzu Zai Aiki a Matsayin TIN ga Mutane, Hukumar Haraji ta Tarayya Ta Sanar da Hakan

TIN
TIN

NIN Yanzu Zai Aiki a Matsayin TIN ga Mutane, Hukumar Haraji ta Tarayya Ta Sanar da Hakan

Daga Sunusi K/Naisa

Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS) ta fayyace cewa Lambar Shaida Ɗan Ƙasa (NIN) da Hukumar Kula da Shaidar Ƙasa (NIMC) ke bayarwa yanzu tana aiki kai tsaye a matsayin Lambar Shaidar Haraji (TIN) ga ‘yan Najeriya a daidaikun mutane.

Hukumar ta bayyana haka ne a ranar Litinin a matsayin wani ɓangare na wayar da kan jama’a kan sabbin dokokin haraji da aka kafa, inda FIRS ta wallafa bayanin a shafinta na X.

A cewar FIRS, wannan gyara na da nufin sauƙaƙa tsarin gudanar da haraji da rage maimaituwar biya fiye ɗaya, da ƙarfafa bin doka ta hanyar amfani da tsari guda na shaida.

Zancen Teburin Mai Shayi: Waye Kai Da Zaka Ce A Janye ‘Yan Sanda daga Nassarawa, Aminu Babba ya Kalubalanci Kwankwaso

Hukumar ta kuma ce kamfanoni da aka yi wa rajista ba za su ƙara buƙatar samun wata Lambar Shaidar Haraji ta daban ba. Maimakon haka, lambar rajistar Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC) ce za ta zama lambar shaidar haraji ga kamfanoni ƙarƙashin sabon tsarin.

FIRS ta lura cewa sabon tsarin an tsara shi ne domin ƙara inganci da inganta haɗa bayanai tsakanin hukumomin gwamnati, da tallafa wa aiwatar da sauye-sauyen haraji da ake ci gaba da yi.

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke nuna damuwa kan wasu tanade-tanaden sabbin dokokin haraji da ke buƙatar Lambar Shaidar Haraji domin wasu mu’amaloli, ciki har da mallakar asusun banki.

A cewar FIRS, Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya (NTAA), wadda za ta fara aiki a watan Janairun 2026, ta tanadi amfani da Lambar Shaidar Haraji ga wasu muhimman mu’amaloli.

Hukumar ta jaddada cewa wannan sharadi ba sabon abu ba ne, inda ta ce tun Dokar Kuɗi ta shekarar 2019 ake amfani da shi, kuma yanzu an ƙara ƙarfafa shi ƙarƙashin NTAA.

“Lambar Shaidar Haraji tana haɗa dukkan lambobin TIN da FIRS da Hukumomin Haraji na Jihohi suka taɓa bayarwa a baya zuwa lamba guda,” in ji Hukumar.

“Ga ɗaiɗaikun mutane, NIN ɗinku kai tsaye yana zama Lambar Shaidar Haraji, yayin da ga kamfanoni da aka yi wa rajista, lambar CAC RC ce ake amfani da ita. Ba kwa buƙatar wani kati, domin Lambar Shaidar Haraji lamba ce ta musamman da ke da alaƙa kai tsaye da shaidar ku.”

FIRS ta bayyana sabon tsarin na da nufin sauƙaƙa hanyoyin gano masu biyan haraji da kawar da maimaituwar biyan da hana gujewa biyan haraji, da tabbatar da adalci ta hanyar tabbatar da cewa duk masu samun kuɗin da ake biyan haraji suna bayar da nasu kason.

NBA Ta Bukaci a Dakatar da Dokar Gyaran Haraji Saboda Kuskurewa Bin Tsarin Doka

Hukumar ta kuma buƙaci jama’a da su yi watsi da duk wani bayani mara tushe game da gyaran, inda ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sabon tsarin haraji an tsara shi ne domin ƙara inganci da bayyana gaskiya a harkar harajin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...