NBA Ta Bukaci a Dakatar da Dokar Gyaran Haraji Saboda Kuskurewa Bin Tsarin Doka
Daga Edita
Read also: NIN Yanzu Zai Aiki a Matsayin TIN ga Mutane, Hukumar Haraji ta Tarayya Ta Sanar da Hakan
Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabbin dokokin gyaran haraji nan take, tana cewa cece-kucen da ke tattare da su na lalata sahihanci da gaskiya da amincin tsarin yin dokar a Najeriya.
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
‘Yancin Ƙananan Hukumomi’: Ku Mutunta Hukuncin Kotun Koli, Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni
A wata sanarwa da Shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe, ya fitar a ranar Talata, 23 ga Disamba, kungiyar ta bayyana damuwa kan yadda aka amince da dokokin, tana mai cewa akwai shakku kan bin ka’idoji da hanyoyin doka.
NBA ta nemi a gudanar da cikakken bincike mai bude ido domin fayyace yadda aka zartar da dokokin da kuma dawo da amincewar jama’a da Majalisar Tarayya.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
’Yan Najeriya 42 Aka Kora Daga Ƙasar Ghana Sakamakon Karuwanci da Aikata Miyagun Ɗabi’u
Kungiyar ta kara da cewa rashin tabbas a doka na iya dagula harkokin kasuwanci, rage kwarin gwiwar masu zuba jari, da barazana ga kwanciyar hankali na tattalin arziki, tana mai kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa domin kare tsarin mulki da bin doka da oda.




























