Connect with us

Hi, what are you looking for?

Kotu

‘Yancin Ƙananan Hukumomi’: Ku Mutunta Hukuncin Kotun Koli, Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu

‘Yancin Ƙananan Hukumomi’: Ku Mutunta Hukuncin Kotun Koli, Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni

Daga Edita

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su bi hukuncin Kotun Ƙoli da ya ba ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu ta fuskar kuɗi, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da ƙin bin umarnin kotun na iya janyo tsoma bakin gwamnatin tarayya.

Shugaban ƙasar ya yi gargaɗin cewa rashin mutunta hukuncin na iya tilasta masa fitar da Umarni na Shugaban Ƙasa (Executive Order) domin tabbatar da biyan kuɗaɗen rabon ƙananan hukumomi kai tsaye daga Asusun Tarayya (Federation Account).

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) karo na 15 na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a Dakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Sule Lamido Ya Yi Gargaɗi Jam’iyyar PDP Na Iya ƙuɗɗa Ƙawance Idan Shugabanci Ya Gaza Warware Rikici

Ya nuna damuwa kan yadda wasu gwamnonin jihohi ke ci gaba da riƙe kuɗaɗen da doka ta tanadar wa ƙananan hukumomi ta hanyar tsarin asusun haɗin gwiwa (joint account), yana mai bayyana hakan a matsayin take haƙƙin hukuncin Kotun Koli.

“ Kotun Koli ta ce a ba su kuɗinsu kai tsaye. Idan kuka jira Umarni na Shugaban Ƙasa, domin ina da wuƙa, ina da doya, zan yanka,” in ji Tinubu, yana mai jaddada cewa haƙurin da yake yi ya samo asali ne daga girmamawa ga gwamnonin.

Kalaman Shugaban Ƙasar sun biyo bayan hukuncin Kotun Koli na ranar 11 ga Yuli, 2024, wanda kotun ta yanke baki ɗaya cewa ba bisa doka ba ne gwamnatocin jihohi su riƙe ko su tafiyar da kuɗaɗen da aka tanadar wa ƙananan hukumomi, tare da umarnin a riƙa biyan su kai tsaye bisa tanadin Sashe na 162 (5–8) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (da aka yi wa gyara).

Rashin Bawa Mata da Kanana Yara Damar Zuwa Asibiti Domin Rigakafi Illa ne Ga Rayuwar Su, In ji Jami’in Lafiya

Yayin da yake jawabi ga mambobin NEC, ciki har da shugabannin Kwamitin Aiki na Ƙasa da sauran jagororin jam’iyya, Tinubu ya sake jaddada cewa bin hukuncin kotun wajibi ne, yana mai cewa girmama hukuncin Kotun Koli muhimmin ginshiƙi ne na tafiyar da mulkin dimokuraɗiyya bisa kundin tsarin mulki.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...