Sule Lamido Ya Yi Gargaɗi Jam’iyyar PDP Na Iya ƙuɗɗa Ƙawance Idan Shugabanci Ya Gaza Warware Rikici
Daga Sunusi K/ Naisa
Read also: An Caka wa Malamin Addini Wuka a Sakkwato, Masu Ibada Sun Kashe Wanda Ake Zargi
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana damuwarsa kan rikicin cikin gida da ke ci gaba da addabar Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), inda ya yi gargaɗin cewa rikicin na iya raunana matsayin jam’iyyar a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya idan ba a gaggauta warware shi ba.
Sule Lamido ya bayyana hakan ne a yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidansa da ke unguwar Sharada a Kano, wanda aka kira sakamakon ƙaruwar damuwar ‘ya’yan jam’iyyar kan rikicin shugabanci a matakin ƙasa da na jihohi.
Alhaji Lamido, wanda shi ma ɗan takara ne a wani matsayi na shugabancin ƙasa na jam’iyyar, ya ce an shirya taron ne domin yi wa masu ruwa da tsaki bayani kan ƙoƙarin da ake yi wajen warware rikicin. Ya bayyana cewa ya fara tattaunawa da gwamnonin PDP da manyan shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaban Kwamitin Sulhu na PDP, Dokta Bukola Saraki, da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da sauran su, domin samo mafita mai ɗorewa ga sabanin da ke cikin jam’iyyar.
Read also: Sarakunan Jama’are Da Ningi Na Miƙa Ta’aziya Bisa Rasuwar Durbin Kano
Gobara ta ƙone Gidan Tsohon Gwamnan a Abuja ƙurmus
A cewarsa, an shirya za a sake zama taro a ranakun Talata da Laraba, inda ake sa ran samun matsaya mafi dacewa. Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su kasance masu haƙuri tare da guje wa duk wani abu da ka iya ƙara hura wutar rikici.
Duk da ƙalubalen da jam’iyyar ke fuskanta, Lamido ya jaddada cewa PDP ita ce kaɗai jam’iyyar adawa mai ƙarfi da za ta iya dawo da daidaiton siyasa, bunƙasar tattalin arziƙi da tsaro a ƙasar nan, yana mai cewa ‘yan Nijeriya da dama na fatan samun sahihiyar mafita mai ɗorewa da za ta fuskanci matsalolin da ƙasar ke fama da su.
Ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki daga Jihar Jigawa cewa dukkan ‘ya’yan jam’iyyar za su samu ‘yancin tsayawa takara a duk wani muƙamin zaɓe da suke so a ƙarƙashin inuwar PDP gabanin zaɓen gama-gari na 2027. Ya ƙara da cewa, duk da cewa ana iya la’akari da yin kawance na siyasa idan ya zama dole, hakan zai kasance ne a matsayin mataki na ƙarshe bayan an gwada dukkan hanyoyin cikin gida na warware rikicin.
Read also: Kwangilar Magunguna: Gwamna Yusuf Ya Ce Bashi Da Masaniya Kuma A Gaggauta Bincike
Da yake jawabi a taron, Shugaban PDP na Jihar Jigawa ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun ziyarci tsohon gwamnan ne domin fahimtar makomarsu ta siyasa da kuma alkiblar jam’iyyar a jihar, la’akari da rikicin da ke ci gaba da addabar PDP.




























