Kwangilar Magunguna: Gwamna Yusuf Ya Ce Bashi Da Masaniya Kuma A Gaggauta Bincike
Daga Wakilinmu
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya musanta zargin da Dan Bello yayi na bayar da kwangilar samar da magunguna a Kananan Hukumomi arba’in da hudu na jihar Kano.
Gwamna ya musanta labarin zargin bayar da kwangilar da aka ce gwamnatinsa ta yi a kwanan nan domin samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 a jihar.
Read also: Mutane 16 Gini Ya Faɗawa A Unguwar Dandishe A Kano
Gwamnatin ta magantu ne cikin wata halakar sanarwa da aka baiwa manema labarai mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye da Sakataren yada labarai na gwamna Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa.
A Karanta Wanna:Al’ummar Unguwar Tarauni Sun Koka Game Da Ambaliyar Ruwa Dake Barazanar Lakume Gidajensu
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan ya umurci Shugaban Hukumar karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano da ta gaggauta bincikar wannan zargi tare da bayar da sahihin rahoton sakamakon da ya dace domin ci gaba da daukar matakin da ya kamata.
Read also: Sule Lamido Ya Yi Gargaɗi Jam’iyyar PDP Na Iya ƙuɗɗa Ƙawance Idan Shugabanci Ya Gaza Warware Rikici
A Karanta Wanna:Akalla Mutane 20 Sun Hallaka Ya Yin Da Suke Tserewa Farmakin ‘Yan Bindiga a Zamfara
Idan za a tuna fitacen masani kafar sada zumunta kuma mai dauke da shedar zaman kasar Amurika da kasar Sin wato Bello Galadanci da aka fi sani da Dan Bello yayi ikirarin cewar gwamnatin Kano ta bayar da kwangilar samar da magunguna ga Kanana Hukumomi 44 na Miliyoyin kudi a kafar sadarwa ta intanet tare da zargin wanda aka bawa kwangilar mai suna Garba Kwankwaso.




























