Akalla Mutane 20 Sun Hallaka Ya Yin Da Suke Tserewa Farmakin ‘Yan Bindiga a Zamfara
Daga Wakilinmu
Read also: An Shiga Firgici Bayan Sabon Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
A kalla sama da mutane 20 ne aka ce sun rasa rayukansu a yankin Kali dake karamar hukumar Gumi a jihar Zamfara a Najeriya, yayin da suke tserewa daga farmakin ‘yan bindiga.
Majiyar STENTORNEWS ta ruwaito cewa mutanan sun hallaka ne bayan hawansu kwale-kwalen domin neman kubuta daga kisan kan-mai-uwa-da-wabi na ‘Yan bindigar, daga bisani kwale-kwalen ya kife a cikin kogi.
A cewar wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun yiwa kauyen kawanya ne da karfe 1:00 na rana a Lahadin da ta gabata.
A Karanta Wanna:Rungumar Sana’a Ce Mafita Ga Matasa, In Ji Pharm. Sule
“Mun ga ‘yan bindigar suna tafiya kauyen Kalli a kan babura dauke da manyan makamai domin kai wa al’ummar hari, lamarin da ya tilasta wa mutanen kauyen tserewa domin tsira da rayukansu.
Read also: Sojojin Najeriya sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 60 a Borno
A cewarsa, kwale-kwalen ya kife ne a kogin Birnin Magaji, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 20.
Ya bayyana cewa an gano gawarwaki biyar a kogin Falale, hudu a kogin Birnin Magaji, yayin da uku kuma aka gano su a kogin gadar Gummi.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun addabi al’umomin Kwammaka, Kwammaka Jibi, Kwammaka Mai Katsina, Kallin da Kazura, duk a karamar hukumar Gummi.
A Karanta Wanna:Gwamnatin Kano Ta Sassauta Dokar Hana Zirga-Zirga
Idan za a iya tunawa wanna ba farau bane a yankin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas, a inda ‘yan bindiga kan yanka kudin fansa domin samun damar gudanar da aikin gona kokuma a matsayin haraji ga al’umma. A sau da dama kin biyan wanna bukatar, mazauna yankin kan hadu da ajalinsu.
Read also: YAN BANGA DA MUTANE 19 SUN RASU A YAYIN ARANGAMA DA YAN BINDIGA A YANKIN DA GWAMNAN BAUCHI YA FITO
Majiyar ta ce an yi kokarin jin ta bakin jami’an tsaro, amma basu ce komai ba. (DIMOKURADIYYA).




























