Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Al’ummar Unguwar Tarauni Sun Koka Game Da Ambaliyar Ruwa Dake Barazanar Lakume Gidajensu

Tarauni
Tarauni

Al’ummar Unguwar Tarauni Sun Koka Game Da Ambaliyar Ruwa Dake Barazanar Lakume Gidajensu

Sakamakon mamakon ruwan sama da ake tafkawa kamar da bakin kwarya a wanna wata na Agusta, mutanan unguwar Tarauni a cikin babban birni jihar Kano sun fara tunanin kauracewa unguwar domin tsira da rayyukansu da kuma dukiya sakamakon barazanar da ambaliyar ruwa yake musu a wanna lokaci.
Ruwan wanda ya kan shiga duk wani sako da lungu na gidajen su domin rashin kyawawan mugudanar ruwa, wanda suka danganta da son zuciya ga wasu suka aikata na gine-gine akan mugudanar ruwa da kuma cushewar su da shara.

Don haka mazauna unguwar ta Tarauni suke neman daukin gwamnatin jihar Kano ta kawo musu agaji na gaggawa don kaucewa asarar rayuka da dukiya.
Malam Huzaifa Isyaku Ibrahim shi ya mika koken ga wakilin jaridar STENTORNEWS, Online a wata ganawa ta hanyar wayar hannu.
Malam Huzaifa ya ce sun fi shekaru goma sha biyar suna fama da matsalar ambaliyar ruwan duk da kokari su na aikin kai-da-kai na sakace magudanar ruwan data taso daga gidan marigayi Sanata Bello Maitama zuwa kasuwar Tarauni ta kuma dire Babban titin Maiduguri.
Ya ce a duk lokacin da suka tsukayi hadari to sun shiga fargaba, domin ruwan cikin gidajensu da kuma dakuna iyalan su yake komawa.

A Karanta wanna:Kungiyar Ci gaban Kampala Sun Cirawa Sanata Ahmed Tagiya Saboda Fitar Dasu Daga Matsanancin Duhu
Magidancin ya koka sosai ” Wallahi duk sanda akai ruwa bamu da kwanciyar hankali, kuma su kansu masu abun hawa sai dai su dakata, in ba haka ba to motoci ko mashin ba su isa su ketare ruwan ba, batare da sun mutu ba”.
Mun yi asarar dukiya mai yawa saboda ambaliyar ruwan tare da kamuwa da cututtuka, mu da iyalanm musamman na cizon sauro da makamantan su, inji Malam Sagir.
Ya yabawa Gwamna Jihar Kano Abba Yusuf bisa umarnin da yayi na kwashe sharar dake kan titin Maiduguri da kuma hana zuba sharar a gurin gaba daya da kuma gyara mugudanar ruwan. Amma ya ce duk da haka a kwai bukatar hukuma data sanya karafuna a bakin kwalabatin domin hana leda toshe mugudanar ruwa gami da kawar da duk gini da a ka yi shi akan mugudanar ruwa.
Huzaifa Sagir, ya kuma roki Ma’aikatar mahalli ta jiha (Environment) da REMASAB da su kawo musu dauki da kuma hana yin gini akan mugudanar ruwa, inda ya danganta hakan a matsayin sanadin matsalar da take addabar su shekara -da-shekaru.
Kamar yadda ya ce sun sanarwa da Ma’aikatar Muhalli da ta Kwashe Shara wato (REMASAB) a rubuce domin su kawo musu gudun mawa, amma hakan ta cittura.

A Karanta wanna:Akalla Mutane 20 Sun Hallaka Ya Yin Da Suke Tserewa Farmakin ‘Yan Bindiga a Zamfara
” Muna rokon gwamna Abba Kabir Yusuf da ya duba kokenmu, kasancewar Tarauni makociyar cibiyar gudanar da mulkin jihar kano ce wato gidan gwamnati.” Inji Huzaifa.

← Back

Thank you for your response. ✨

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...