Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Mazauna Kusa Da Madatsar Ruwa ta Ghari Da Su Yi Nesa Da Kogi – Inji Shugaban Ƙaramar Hukuma

Jihar Kano Ghari
Jihar Kano Ghari

Mazauna Kusa Da Madatsar Ruwa ta Ghari Da Su Yi Nesa Da Kogi – Inji Shugaban Ƙaramar Hukuma

Daga Sunusi K/Na’isa

A yayin da damina take kankama, Hukumar kula da yanayi ta ƙasa ta bada sanarwar yuwar samun ruwan sama mai yawa musamman a jihohi Arewa shida ciki har da jihar Kano a waɗannan kwanaki, haka kuma ana fargabar samun ambaliyar ruwa a madatsun ruwa daban-daban wanda Ƙaramar hukumar Ghari na daga cikin su a jihar Kano, Shugaban ƙaramar hukumar Ghari Alh. Hashimu Garba Mai Sabulu ya gargadin al’ummar dake dab da madatsun ruwa da su kaucewa guraran.

Shugaban ya miƙa saƙon gargadin ta hannun Jami’en Yaɗa labarai na yankin, Shibili Rabi’u S/Titi.

Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11

Shugaban Ƙaramar hukumar ya ja hankalin mazauna yankunan da su ke kusa da madatsar ruwa ta Ghari da su janye jikinsu har zuwa wani lokaci domin kaucewa asara rai ko dukiya.

Ya ce garuruwan da barazanar ambaliyar ruwa ka iya shafa sun haɗar da, Gobirawa da Duku da Galadimawa da Shamakawa da Burgumawa da kuma garin Korafawa.

Shugaban na Ghari ya ce tuni ƙaramar hukumar sa ta ɗauki matakin kar ta kwana na gaggawa domin kaucewa ambaliyar ruwan da kuma samar da kariya idan har ta faru, game da kira ga jama’a da su tsaftace magudanar ruwan su a dukkanin sako da lunguna.

Hak kuma ya bukaci Dagatai da masu Unguwanni da su cigaba da faɗakar da al’ummar yankin musamman makwabta da madatsar ruwan ta Ghari domin isar da sako.

Ambaliya ruwa ta hallaka mutane sama da 100 a jihar Texas ta Amurka
Don haka ya yi addu’a ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya bada damina mai albarka kuma ya kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma samun abinci wadatacce.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...