SHUGABAN MUSLIM UMMAH NA KASA PROF. MOHAMMED BABANGIDA GAMAWA YA GODEWA JIHOHIN BAUCHI DA YOBE.
Daga Muazu Hardawa, a Damaturu
Shugaban kungiyar Muslim Ummah mai rajin bibiyar matsalolin da musulmi da musulunci ke fiskanta a Nigeria domin neman yadda za a magance su, ya yaba wa jihohin Bauchi da Yobe game da kokarin su na daukar nauyin tarukan kungiyar da suka gudana a jihohin su.
Prof. Babangida Gamawa Malami a Jamiar Bayero da ke Kano ya bayyana haka ne a wajen taron shiyyar arewa maso gabas da ya gudana a garin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe na tsawon kwanaki uku.
Yace addinin musulunci baya tsufa don haka ya zamo wajibi a habaka rayuwa a gina al’umma a kan adalci don a zamo abin koyi kamar yadda Allah ya umarci musulmi.
Don haka ya ce tafiyar Muslim Ummah aiki ne babba da kowa ya kamata ya fito don bayar da gudummowa da shawarwari masu kyau ga hukumomi da Jama’a don tabbatar da adalci wa mutane da ake jagoranta.
Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai
Saboda a halin yanzu babu abin da ke saurin rusa al’umma kamar zaluncin shugabanni, don haka matukar aka samu gyara daga sama.kowa zai gyara a kasa.
Saboda haka ya ce aikin kungiyar Muslim Ummah shine hada kai da kungiyoyi da daidaikun Jama’a don kowa ya sadaukar da kansa a samu gyara a ciyar da musulmi da musulunci gaba.
Ya kara da cewa musamman a wannan lokacin da turawa suka sa musulmi a gaba ana kalubalantar su a kan suna kashe kiristoci a Nigeria, alhali kullum musulmi ake kashewa, haka kuma magoya bayan kowace akida suna fiskantar wannan matsalar.
Professor Babangida Gamawa ya kara da cewa kungiyar Muslim Ummah tana tare da kowace kungiya don kawo ci gaban musulmi.
Don haka akwai tsare tsaren musulunci da ake bi ba tare da wuce gona da iri ba don kawo ci gaba a fannin inganta rayuwar mutane.
Don haka ya bukaci kowa ya himmatu wajen samun Ilmi ta hanyar fito da kwararru da suka dace a kowane fannin addini da rayuwa don a samu tasirin tarbiyya.
Matukar mutane suka rasa Ilmi da tarbiyya da jagoranci na adalci komai zai Iya rushewa.
Yace akwai tsari na tafiyar da aiki da majalisar Shura da kuma shugabanni da ma’aikatan ofis da masu bincike da ake da su don cimma manufa da aka sa a gaba, tare da karfafa yadda za a shigo da kowa cikin tafiyar don samun hanyoyin kudin shiga don ganin ba a dogara kan yin bara a tsakanin Jama’ar musulmi ba kafin a samu gudanar da ayyukan kungiyar ba.
Read also: Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Karin Girma ga Malaman Makaranta 16,634.
Daga karshe ya Muslim Ummah da Shura sun samo asali daga daga kungiyar dalibai ta MSS sama da shekaru 70 da suka gudana.
Kuma haka aikin ke tafiya Har zuwa yanzu da ake bukatar kowa ya shigo ya bayar da gudummowa.




























