Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Karin Girma ga Malaman Makaranta 16,634.

Gov Abba

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Karin Girma ga Malaman Makaranta 16,634.

Daga Wakilinmu

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da yi wa Malaman Makaranta da sauran ma’aikatan sassan ilimi na Kananan Hukumomi 44 su 16,634 karin girma (Promotion).

Bayanin hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da Daraktan Sashen Lura da Harkokin Sadarwa na Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB), Balarabe Danlami, ya fitar.

Daraktan ya bayyana cewa Shugaban Hukumar SUBEB, Malam Yusuf Kabir, ne ya sanar da wannan albishir yayin da yake jawabi kan batun karin girman, inda ya tabbatar da amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf na biyan dukkan kudaden da suka shafi karin girman.

An Yi Kira ga Karamar Hukumar Sumaila da ta Samar da Bandaki a Makarantar Liman Yau JASS Sumaila

A cewarsa, Malaman Makaranta da sauran ma’aikatan sassan ilimi 16,634 ne suka amfana da wannan karin girma, wadanda lokacin karin girman nasu ya kama daga watan Yulin 2024 zuwa watan Yulin 2025.

Shugaban Hukumar ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano bisa wannan gagarumin tagomashi, yana mai cewa hakan na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na bunkasa walwalar ma’aikata da kuma inganta harkar ilimi.

Fiye da Musulmi Miliyan Uku Sun Hallara a Katsina don Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse

Daga bisani, ya yi kira ga Malaman Makaranta da sauran ma’aikatan da suka amfana da wannan karin girma da su kara jajircewa wajen gudanar da ayyukansu, domin taimakawa Gwamnati wajen cimma kudurinta na inganta ilimi a fadin Jihar Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...