Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

SUBEB DA UNICEF DA UBEC SUN KADDAMAR DA GANGAMIN SA YARA MAKARANTA A BAUCHI 

Jihar Bauchi
Jihar Bauchi

SUBEB

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

A kokarin gwamnatin jihar Bauchi na ganin an ja hankalin iyaye don sanya yaran su a makaranta, gwamnatin jihar Bauchi da hadin guiwar hukumar Ilmi a matakin farko ta tarayya UBEC da hukumar lura da yara ta majalisar dinkin duniya sun kaddamar da shiri don jan hankali da wayar da kan jama’a don sanya yara a makaranta.
Shirin an kaddamar da shi ranar juma’a 5/9/2025 a dakin taro na GDSS Kirfi, a jihar Bauchi, yadda mutane da dama suka samu halarta.
Cikin jawabinsa bayan bude taron da adduah, shugaban karamar hukumar kirfi Alhaji Abdulkadir Umar Dewu, ya yaba game da basu damar daukar nauyin gudanar da shirin na matakin jiha. Don haka ya ce wannan babban lamarine gare su na kawo babban aiki irin wannan a karamar hukumar kirfi, musamman ganin yadda karamar hukumar ke fama da samun karancin sanya yara a makaranta akwai koma baya a Yankin sa na Kirfi.
Yace amma a yanzu an samu ci gaba, saboda a baya akwai lokacin da Idan aka bukaci a kawo dan takarar kansila mai takardar Sakandare ingantacciya don takarar kansila a wasu yankunan ba a samu, amma a yanzu irin wannan kokari na wayar da kai da gwamnatin jihar Bauchi ke Yi ya sa ana samun sauyi.

Ga Wasu Labaran:

Haka kuma a yanzu an fahimci muhimmanci da tasirin Ilmi saboda a yanzu hatta noma sai an yi ta da Ilmi kafin a samu abin da ake nema na wadata kasa da abinci.
Hon. Abdulkadir Dewu ya kara da cewa lokaci yayi da za su ba Ilmi muhimmanci a fito a sa yara a makaranta. musamnan daga kasa cikin yankunan karkara akwai matsala, saboda akwai lokacin da matar Gwamna ta turo tawaga yankin karamar hukumar kirfi suka je wani gari sun tara kusan yara dari amma guda biyu suka samu suna karatu a firamare.
Don haka Hon. Abdulkadir Dewu ya bukaci iyaye da shugabanni da limamai su fito su bayar da gudummowa don jan hankalin jama’a su sa yara a makaranta. Kuma a nuna musu muhimmancin manyan Frofesosi ‘yan Yankin kirfi da ke aiki a manyan wurare ciki har da babban asibitin koyarwa na ATBUTH da ke Bauchi shugaban sa Profesa Yusuf Jibrin Bara dan kirfi ne.
Haka a manyan ma’aikatu da jami’o’in Nigeria da kasashen duniya akwai Yan yankin kirfi da ke aiki kuma duk Ilmi ne ya kai su.
Shugabar hukumar UNICEF a Jihar Bauchi Madam Nughat Rafique a matsayin ta na wacce suka tallafa wajen kaddamar da shirin a sakon ta na fatar Alheri, ta ja hankalin iyaye su kai yaran su makaranta don magance duk wani kalubale na lalacewar tarbiyyar da rashin Ilmi ke haifarwa kamar yadda ake amfani da matasa jahilai wajen kunna wutar fitina a kasashen duniya.
Profesa Bala Dalhat Sulaiman na Jamiar ATBU a matsayin sa na bako mai jawabi ya bayyana illolin rashin kai yara makaranta da Kuma yadda za a taimaka a magance matsalolin jahilci da illolin da rashin Ilmi ke haifarwa a cikin al’umma DA kuma koma baya da ake samu.
Hukumar bunkasa Ilmi a daga tushe ta tarayya UBEC sun taimaka wajen daukar nauyin gudanar da gangamin, Alhaji Abdullahi Shehu Jarma na ofishin hukumar da ke Bauchi, shine ya wakilci Sakatariyar hukumar ta kasa Hajiya Aisha Garba, a cikin jawabinsa ya bayyana kokarin gwamnatin tarayyar Nigeria na tallafawa hukumomin Ilmi don ganin an kai yara makaranta saboda sune za su kasançe manyan gobe da za su rike ragamar gudanar da kasa, don haka ya ja hankalin masu Unguwanni da sarakuna da malaman addini su taimaka wajen wayar da kan iyaye don kai yaran su makaranta saboda a samu nasara kan aikin da gwamnati ta sa gaba don ilmantar da yara saboda su samu makoma ta gari.
Dr. Nasir Ala Chinade shugaban kwamitin Ilmi a majalisar dokokin jihar Bauchi cikin jawabinsa ya ja hankalin iyaye su fahimci muhimmancin Ilmi ya wuce duk yadda suke zato, yadda ya bayar da misali da shi kansa iyayen sa mahauta ne amma karatu ya kai shi matsayin Dokta yana koyarwa a manyan makarantu daga bisani mutanensa suka zabe shi dan majalisar dokokin jihar Bauchi yanzu yake Wakilin Chinade da Madara ya bar sana’ar fawa kuma Ilmi ya fito da shi duniya ta san da zaman sa.
Don haka ya bukaci mutane su gujewa tafiya neman ma’adinai a daji su kai yaran su makaranta saboda a karshe za su iya zama kowane irin matsayin da suke so a duniya Idan suna da Ilmi.
A matsayin sa na babban bako Na musamnan a wajen taron, kwamishinan Ilmi Na jihar Bauchi Dr Lawal Muhammad Rimin Zayam ya bayyana kokarin gwamnatin jihar Bauchi na gina makarantu da samar da kayan aiki a kowane sashe na jihar Bauchi anma iyaye basa son kai yara makaranta, musamnan a yankunan karkara, yadda bata gari ke lalata makarantun da kayan aiki, duk da makudan kudi da ake kashewa domin ilmantar da yara saboda gwamnati ta sauke nauyin da ke Kanta.
Kwamishinan ya godewa gwamnatin Sanata Bala Mohammed Abdulkadir na ganin irin kokarin da take Yi don inganta Ilmi a jihar Bauchi, don haka ya ja hankalin iyaye da sarakuna da malaman addini a taimaka a wayar da kan iyaye don su kawo yara makaranta su yi karatu kyauta su amfana.
Shugaban hukumar Ilmi a matakin farko ta jihar Bauchi SUBEB Alhaji Adamu Mohammed Duguri wakilin Bauchi Hakimin kasar Duguri, shine ya jagoranci gudanar da taron, yadda a cikin jawabinsa ya bayyana takaici game da sakacin iyaye da wasu Malaman makarantu game da rashin ilmantar da yara kamar yadda ake so. Don haka ya ja hankalin malamai da shugabannin makarantu kowa ya rike aikin sa tsakani da Allah.
Yace ya bayar da umarnin shugabannin kananan hukumomi da Sakatarorin Ilmi su hukunta dukkan malaman da suka gaza sauke amanar da aka dora musu na karantar da yara a makarantu.
Yace akwai malamai marasa kishin da aka samu da laifin lalatawa da sace kayan makarantu suna kaiwa bola jari Kuma tuni an hukunta su don haka a shirye hukumar sa take wajen ganin ta hukunta dukkan masu sakaci da aikin su.
Alhaji Adamu Mohammed Duguri ya ce gwamnatin jihar Bauchi ta shirya tsaf wajen zama abin misali a fagen Ilmi. Don haka ya zamo wajibi kowa ya tashi tsaye don sauke nauyin da ke kansa game da ilmantar da mutane da Allah ya bashi Amana
Tuni dai dukkan shugabanni da suka halarci taron da Wakilin maimartaba Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Sulaiman Adamu suka kaddamar da yin rijistar yaran a makaranta tare da raba musu kayan aiki da suka kunshi littafai da kayan makaranta da sauran su kyauta.
Kuma Daga wannan rana Alhaji Adamu Mohammed Duguri wakilin Bauchi Hakimin kasar Duguri ya bukaci dukkan kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi su ci gaba da rijistar yara a makarantar nazare da firamare da Sakandare kanana da manya don ganin an samu nasarar inganta shirin gwamnati na ilmantar da yara a dukkan fadin jihar Bauchi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...