Gwamnatin Kano ta Sanar da Ranar konawa Makaranta
Daga Sani Aminu
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Ziyarartar Makarantun Kwana
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar komawa makarantun firamare da na sakandare domin cigaba da darasun sabon zangon karatu na shekarar 2025/2026.
Read also: Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun 8 masu zaman kansu
A wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi,ta Kano, Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar ta bayyana cewa, ɗaliban makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi, 7 ga watan Satumba, 2025, yayin da ɗaliban makarantu na jeka ka dawo za su koma a washegari Litinin, 8 ga Satumba, 2025.
Wasu Labaran:
- Gobe Litinin Ita Ce 1 Ga Watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira, In ji Sarkin Musulmi
- Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
- Haramtacciyar Harkar Ma’adanai Ke Rura Wutar Ta’addanci A Najeriya, Kuma Wasu Manyan Mutane Ke Gudanarwa
Read also: Auren Gata Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne, Inji Sheik Hadi MaiHula
An shawarci iyaye da masu kula da yara su kula da wannan jadawalin domin tabbatar da cikakken bin doka, inda aka gargaɗi ɗalibai da suka saba dokar cewa za su fuskanci hukunci mai tsauri.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ya yi fatan alheri ga malamai da ɗalibai wajen sabon zangon karatu mai kamawa.



























