Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar

Shugaban Burkina Faso na soji Ibrahim Tarore hoto(DPL Daily)
Shugaban Burkina Faso na soji Ibrahim Tarore hoto(DPL Daily)

Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar

Dada Sunusi K/Na’isa

Ƙasar Burkina Faso ƙarƙashin jagoranci Ibrahim Tarore ta kori shugabar dake kula da sashin ayyukan jinƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya Carol Flore-Smereczniak daga ƙasar, dangane da wasu rahotanni da ta fitar dake zargin ƙasar dake yammacin Afirka da take hakkin ƙananan yara.

Mai magana da yawun gwamnatin Burkina Faso ya bayyana cewa babu wanda ya tuntuɓi mahukuntan ƙasar akan wannan rahoton da jami’ar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta wallafa akan zargin dake cewa ƙasar na cusa yara ƙanana a cikin mayakanta.

A waje ɗaya kuma, Gwamnatin Burkina ta zargi Majalisar Ɗinkin Duniyar da shirya wasu bayanai marasa tushe balle makama a cikin rahotanninta, ba tare da ta gudanar da sahihan bincike kuma tabbatar da nagartar bayanan da ta samu kafin ta wallafa ba.

Dangane da korar da Burkin Fason ta yi wa shugabar ayyukan jinƙan ta MDD aƙasar, ya zuwa yanzu dai babu wani furuci da aka samu daga jami’an Majalisar a ofisoshinsu na Geneva da New York na ƙasar Amurka.

RFI, ta ruwaito cewa, wannan na zuwa ne a yayin da tashe-tashen hankula da aka shafe shekaru goma ana gwabzawa da masu ikrarin jihadi da ke da alaka da Al Qaeda da IS ya ƙara muni, lamarin da ya sa Burkina Faso da kasashen dake makwabtaka da ita suka yi juyin mulki a ɗaya bayan ɗaya daga 2020 zuwa 2023.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...