Ma’adanai
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya
Hukumar rundunar ‘yan sanda Najeriya ta ce hada-hadar harkar haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ita ce ummul-abaisun rura wutar ta’addanci a ƙasar wanda kuma hakan ke zama sanadiyar tafka gagarumar asarar kuɗaɗen shiga ga ƙasar.
Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Ajao Adewale, ya bayyana haka a wani taron wayar da kan ‘yan jarida kan illolin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
“Haramtacciyar hakar ma’adinai ta zama babban kalubale ga tsaron Najeriya, kuma ta na daga cikin manyan hanyoyin da ke rura wutar ayyukan ta’addanci,” in ji Adewale.
Ya ce “Kuma babban takaicin akwai wasu fitattun mutane masu faɗa a ji a ƙasar da ke ɗaukar nauyin ta’addanci da garkuwa da mutane da gudanar da hada-hadar haramtacciyar hakar ma’adinai”.
Read also: Mutane 5 sun mutu da yawa sun jikanta sakamakon fashewar bom a Kano
Hukumar NEITI da ke sa ido kan harkar albarkatun ƙasa ta tabbatar cewa Najeriya na asarar kusan dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon fasaƙwairin zinare da sauran albarkatun ƙasa daga Najeriyar.
Hukumar ta kara da cewa wannan aiki na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na lalata muhalli da karya dokokin ƙasa da hana masu zuba jari, da kuma bayar da tallafi ga ayyukan ta’addanci.
Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan mutane a Najeriya ke da hannu kai tsaye wajen ɗaukar nauyin wannan aiki, inda suke amfani da ‘yan ƙasashen waje wajen aiwatar da shi. Haka kuma ana amfani da ‘yan bindiga wajen kare ayyukan don kaucewa bincike ko hukunci.
Adewale ya bayyana jihohin Zamfara, Nasarawa, Kogi, Kaduna, Neja, Kwara, Osun da kuma wasu sassan Abuja a matsayin wuraren da ake yawan gudanar da wannan haramtacciyar hakar ma’adinai.
Read also: Amurka ta Kai Wani Mummunan Hari Kan IS a Najeriya, In ji Trump
Ya ce daga shekarar 2023 zuwa 2024, rundunar ta kama mutum 72 da ake zargi da hannu a irin wadannan ayyuka, inda ya kara da cewa jami’an tsaro za su ci gaba da ɗaukar matakai na musamman domin daƙile wannan barazana.
FRI HAUSA




























