Babban Yaron Ɗan Ta’adda Bello Turji, Yalo Ɗan Bokolo ya Baƙunci Lahira
Rahotanni na nuni da cewa an hallaka babban ɗan uwa ga Bello Turji kuma babban Yaron sa, Yalo Ɗan Bokolo a Ƙaramar Hukumar Shinkafi.
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Ɗan Bokolo, ɗan uwa ne ga shahararren ɗan bindiga Bello Turji, ya mutu bayan samun wata lugudan wuta da harbin bindiga a wata arangama mai zafi dashi da Jami’an tsaron gari.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa gidan talabijin na AIT News cewa a ƙalla mayaƙan sa 173 sun mutu a wannan hari wanda mazauna yankin suka bayyana a matsayin “babbar nasara da ba’ayi tsammani a nan kusa ba”, kuma shi ne mafi munin hari a tarihin yaƙi da ƴan bindiga a wannan yanki.
A karanta:Hafsan Sojoji Burtai Ya Kai da Kyar Sakamakon Harin ‘Yan Boko Haram A Borno
Duk da cewa Hukumar Tsaro ta DSS ba ta tabbatar da rawar da ta taka ba, wasu majiyoyi sun ce hukumar ta bayar da gagarumin goyon baya ta fuskar bayar da bayanan sirri a lokacin da za a kai harin.
A gundumar Kurya da wasu ƙauyuka da ke maƙwabtaka da ita, al’umma sun fara murna da shagulgula da jin samun labarin nasarar da tai sanadiyyar kisan shahararren ɗan ta’addan.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Manoma da mazauna yankin na murnar kawo ƙarshen zaman fargaba da biyan harajin da ba gaira ba bu sabar da kuma hare-haren kisan gilla da suka daɗe suna fuskanta.
Ɗan Bokolo, wanda ake ɗauka a matsayin gwarzon jagoran ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yamma, ana ganin shi ne ke tsara hare-hare, yayin da Turji ke matsayin mai magana da yawunsu.
Mazauna yankin sun ce magoya bayan Turji sun shiga ruɗani, tare da rahotanni da ke nuna cewa wasu daga cikinsu na neman afuwa yayin da rundunonin tsaro ke ƙara matsa lamba.
Wannan shi ne karon farko da ƴan bijilanti suka kai hari kai tsaye kan sansanin Turji tun bayan da ta’addanci ya mamaye yankin.
Al’umma sun bayyana fatan su na samun damina ta noma da za ta kasance babu haraji ko tsoro, tare da nuna godiya ga gwamnatoci kan ba yar da goyon baya ayaƙi da ta’addanci.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Mutuwar Ɗan Bokolo, na iya zama babban ci gaba a yaƙin da a ke yi da ta’addanci a Arewa maso Yamma.
Amma har ya zuwa haɗa rahoton bamu sami wata sanarwar daga jami’en tsaro na soji ba dangane da tabbacin kashe ƙassurgumin ɗan ta’dda Ɗan Bokolo.




























