Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Hafsan Sojoji Burtai Ya Kai da Kyar Sakamakon Harin ‘Yan Boko Haram A Borno

Hafsan sojojin Ƙasa Yusuf Tukur Burtai rtd
Hafsan sojojin Ƙasa Yusuf Tukur Burtai rtd

Hafsan Sojoji Burtai Ya Kai da Kyar Sakamakon Harin ‘Yan Boko Haram A Borno

Daga Adita

Tsohon Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya tsallake rijiya da baya a ranar Juma’a, bayan da motocin da ke dauke da shi da rakiyarsa suka gamu da harin bindiga daga ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan ne suka kitsa harin a kusa da wata sansanin soja da ke yankin gaba da fagen fama, inda suka bude wuta kan tawagar da ke tare da tsohon hafsan.

A Iya Karanta Wanna:Dangote Ya Sanya Wa Hanya Suna Tinubu, Zai Kashe N900 Biliyan Don Gina Hanyoyi A Najeriya

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a daren Lahadi.

A cewarsa, harin ya kara dagula lamarin tsaro a yankin Arewa maso Gabas, wanda ke ci gaba da fama da hare-haren Boko Haram da na ‘yan ISWAP.

Ndume ya ce dakarun da ke rakiya Buratai sun mayar da martani cikin jarumta, inda suka shiga musayar wuta da ‘yan ta’addan, duk da cewa an samu barna a bangaren kayan aiki.

“Muna cikin wani mawuyacin hali na tsaro. Kwanaki biyu da suka gabata, an kai hari kan Laftanar Janar Buratai a kusa da wani sansanin soja da ke gaba da fagen fama. Sai dai dakarun sa sun nuna jarumta wajen dakile harin, kodayake ‘yan ta’addan sun lalata kayayyakin yaki da dama,” in ji Ndume.

A Iya Karanta Wanna:Boko Haram: Zulum ya bayar da gudummawar N30m ga iyalan hafsan sojojin da aka kashe, Alari

Sai dai har zuwa yanzu babu rahoton asarar rai da aka tabbatar a harin.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara fuskantar kalubale na tabarbarewar tsaro a wasu yankunan Arewa maso Gabas, lamarin da ke kara sanya damuwa cikin zukatan al’ummar yankin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...