Amurka ta Kai Wani Mummunan Hari Kan IS a Najeriya, In ji Trump
Daga Edita
Read also: Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya
Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya ce Ma’aikatar tsaron Amurka ta Kai harin soji da makami mai linzami da aka harbo daga jirgin ruwa sojin Amurka ga ‘yan ta’addan ISIS dake Najeriya a daran Alhamis.
A wani gajeren bidiyo da Ma’aikatar tsaron Amurka ta wallafa da ke nuna wani harin makami mai linzami da aka harbo daga wani jirgin ruwan soji Asalin hoton, (US Department of Defense).
’Yan Najeriya 42 Aka Kora Daga Ƙasar Ghana Sakamakon Karuwanci da Aikata Miyagun Ɗabi’u
BBC Hausa ta ruwaito, Shugaba Trump ya ce Amurka ita ta ƙaddamar da wannan mummunan hari kan mayakan IS a arewa maso yammacin Najeriya.
“Dakarun Amurka sun ƙaddamar da hare-hare masu kyau,” in ji Trump.
Read also: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya
Cibiyar sojin Amurka a Afrika daga baya ta ce an kai hare-haren ne a jihar Sokoto.
Shugaban ya zargi kungiyar da kai hari tare da kashe kiristocin da ba su ji ba su gani ba a kasar.
Sakataren harkokin tsaron Amurka Pete Hegseth, ya ce ya gamsu da haɗin kai da kuma goyon bayan da gwamnatin Najeriya ta ba su wajen samun nasarar kai harin.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce harin wani ɓangare ne daga cikin haɗin gwiwar tabbatar da tsaro da aka ƙulla da Amurka.
A watan Nuwambar da ya gabata shugaba Trump ya bayar da umarni ga rundunar sojin kasarsa ta shirya ɗaukar mataki kan Najeriya domin magance mayakan ƙungiyar na ISIS.
Read also: Sojoji Sun Daƙile Hari Yan Bindiga A Kano
Ƙirƙirar Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Ya Saɓawa Doka, In Ji Farfesa Mai Bushira
Ya yi zargin ana yi wa kiristoci kisan ƙare dangi, abin da gwamnatin Najeriya ta musanta tare da watsi da iƙirarin nasa



























