‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya
‘Yan bindiga sun sace ma’aikatan jinya a wata cibiyar kula da lafiya a matakin farko da ke kauyen Layin Dan Auta, Mazabar Kuyello, yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna.
Read also: Sojoji Sun Daƙile Hari Yan Bindiga A Kano
Kamar yadda majiya ta sheda mana wacce ta nemi mu boye suna, an ce ainihi sun kai hari ga makarantar firamare dake yankin, sai dai kuma sun iske babu dalibai, sai suka zarce zuwa cibiyar lafiya da ke kusa. Kuma suka yi garkuwa da ma’aikatan jinya da ke bakin aiki a wani matsakaicin Asibiti.
Wani shugaban al’umma da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin tsoro. “Sun isa makarantar amma sun iske babu kowa a ciki. Daga nan suka koma cibiyar kula da lafiya a matakin farko suka dauki ma’aikatan jinya,” in ji shi.
Read also: Yadda Laftanar AM Yarima ya tsallake harin ‘yan bindiga
A Karanta Wanna:Ƙasurgumin Dan Dabar Da Ya Addabi Jama’a A Kano Burakita Ya Sheka Barzahu
Baba Isah, wani shugaban matasa a Kuyello, shi ma ya tabbatar da sace ɗaliban. Ya ce ma’aikatan jinya biyu na wurin a lokacin da aka kai harin, kuma har yanzu babu tabbas kan ko an sace wasu marasa lafiya, kamar yadda mafi yawa suka bar wurin kafin a kai samamen.
Har zuwa lokacin wannan rahoto, babu wani bayani a hukumance daga gwamnatin jihar ta Kaduna ko kuma ‘yan sanda.
Read also: Amurka ta Kai Wani Mummunan Hari Kan IS a Najeriya, In ji Trump
A Karanta Wanna:Zamfarawa Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 37 A Kokarin Kwatar Kai
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura.
Daily trust



























