Sojoji Sun Daƙile Hari Yan Bindiga A Kano
Daga Wakilinmu
Read also: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya
Dakarun rundunar haɗin gwiwa sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin kai hari da ‘yan bindiga suka yi a wasu al’ummomi a yankin ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano bayan wani dogon lokaci na musayar wuta.
Rikicin, wanda ya fara a daren jiya Alhamis kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Juma’a, ya faru ne a ƙauyukan Yankwaɗa, Babanduhu, da sauran kauyukan da ke maƙwabtaka da yankin.
Read also: Hafsan Sojoji Burtai Ya Kai da Kyar Sakamakon Harin ‘Yan Boko Haram A Borno
Da yake tabbatar da lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Kakakin Rundunar Sojin Najeriya a Kano, Maj. Zubair Babatunde, ya ce ‘yan bindigar sun yi yunƙurin mamaye al’ummomin a kan babura yayin da suke harbi.
Read also: Sojoji Sun Lakume Manyan Kwamandojin Bello Turji Guda 7, Da Sauran Yaransa 24
Kyautata Zamantakewar Aure: Kungiyar Anwarul-Qalam Bauchi ta Horas da ‘Yan Mata 100
Babatunde ya ce harin wani ramuwar gayya ne bayan rasa wasu daga cikin mayaƙan ‘yan bindigar waɗanda sojoji suka hallaka a wata fafatawa da suka yi a makon da ya gabata.



























