Gwamna Bala Mohammed Ya ce Yaiwa Jam’iyyar PDP Zuwan Sojan Badaskare, Duk da Bita-da-kuɗin Da Ake Masa
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Tsohon Gwamna Jigawa Sule Lamido Ya ce Zasu Samawa Jam’iyyar PDP Mafita Kwanana
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya zargi Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike da wasu yan siyasa a sama da yunkurin bata masa suna da lalata mutuncinsa da na iyalan sa a idon duniya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke hira da manema labarai a gidan gwamnati, bayan ya sanya hannu a kasafin kuɗi da aka gabatar masa.
Ya ce ana ta yi masa bita da ƙulli da jifa da zarge-zarge marasa tushe, ciki har da alakanta shi da batun ta’addanci da ‘yan bindiga, lamarin da ya musanta.
Kyautata Zamantakewar Aure: Kungiyar Anwarul-Qalam Bauchi ta Horas da ‘Yan Mata 100
Read also: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Dongwarar da Jam’iyyar NNPP
Ina ji Gwamna, ana alaƙanta shi da ta’addanci tare da shugaban fulani Alhaji Badejo alhali kowa ya san ƙoƙarin sa na siyasa wajen haɗa kan Fulani har suka zabi Bola Tinubu da Gwamnan Nasarawa da sauran ‘yan siyasa manya a ƙasar nan.
A cewarsa, Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewa maso Gabas, kuma hakan ya samu ne ta hanyar hikima da dabaru da adduah da ya ke yi. Amma duk da rigar kariyar mulki da yake da ita ba tare da jin tsoron Allah ba ana alaƙanta shi da laifuka na ta’addanci.
Gwamna Bala Mohammed ya ce ana yi masa haka ne saboda yana daga cikin manyan ‘yan adawa a Najeriya duk da irin ayyukan alheri na gina ƙasa da ya ke yi amma ana yi masa yarfen siyasa.
” Jami’an tsaro da DSS sun san masu aikata miyagun ayyuka amma suna kallo ba a tsangwamesu ba sai ni da nake aiki don gina jihar Bauchi da mutanenta”, in ji Bala Mohammed.
Don haka yana nan daram a jamiyyar PDP da mutanen sa babu wata barazana da za ta sa ya koma APC har abada.
Gwamna Bala Mohammed ya kuma ce zai kare kansa a dukkan matakai, yana mai cewa ya riga ya rubuta wa Babban Lauyan gwamnatin Tarayya tare da sanar da hukumomin tsaro, kuma zai kai ƙorafinsa ga ƙasashen duniya saboda abin da ya kira tauye masa ‘yancin dan Adam da na siyasa yadda don tozarci an sa EFCC ta kama kwamishinan kuɗin sa ta kuma tsare saboda son zuciya.
Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana kewaye da mutane da ke neman cutar da shi a siyasa, yana mai cewa Ministan FCT, Nyesom Wike, “ba cikakken mamba ba ne na jam’iyyar PDP,” kuma yana janyo wa jam’iyyar cikas.
Read also: Kotin ƙoli: Nura Husaini Ya Bayyana Nasarar Gwamna Abba A Matsyin Nasara Ga Al’ummar Kano
Duk Wanda Ya Tafi Jam’iyyar APC ya Tafi Shi Kaɗai, In ji Sanata Rufai Sani Hanga
A saboda haka ne Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Ƙaramar Hukumar Katagum ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan suka da yarfen siyasar da Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC da kuma EFCC ke yi na ƙoƙarin ɗora Gwamna Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, na cewa yana da hannu ko ɗaukar nauyin ta’addanci.
Wannan zargi ba shi da tushe balle makama, ƙarya ce tsagwaronta, kuma yunƙuri ne na siyasa da aka shirya domin ɓata sunan Gwamna Bala Muhammad, wanda duniya ta sani a matsayin sa na shugaba mai kishin al’umma, mai jajircewa wajen yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in rashin tsaro a Jihar Bauchi da ma Arewa gaba ɗaya.



























