Kyautata Zamantakewar Aure: Kungiyar Anwarul-Qalam Bauchi ta Horas da ‘Yan Mata 100
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Aƙalla Ɗalibai Mata Dubu 12,133 Zasu Sami Tallafin Karatu Na AGILE A Bauchi
Domin magance matsalolin da ake fuskanta na lalacewar zamantakewar aure a jihar Bauchi, wata ƙungiya mai sun Anwarul qalam foundation ta shirya taron bita na tsawon kwanaki hudu ga yan mata da zawarawa masu aure ko masu shirin yin aure don ilmantar da su ladubban zaman aure da suka shafi tsabta da ladabi da dogaro da kai da sauran su.
Taron na kwanaki hudu ya gudana a makarantar Kobi da ke Bauchi, don a magance matsalolin da ke faruwa tsakanin ma’aurata, yadda bisa al’ada duk lokacin ƙarshen shekara zuwa azumi da bukukuwan sallah ana samun yawaitar yin bukukuwan auren ‘yan mata da zawarawa, amma kuma daga bisani akan samu sabani yadda auren ke lalacewa a wasu gidajen.
Don haka ne wannan ƙungiyar ta himmatu wajen ganin an shirya taron wayar da kai da ake kira Daura a harshen larabci. ‘yan mata da zawarawa da dukkan masu sha’awa ma’aurata ko masu shirin yin aure don ilmantar da su ginshikan zamantakewar aure ne suka haɗarci taron.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Kaɗu Matuƙa Da Rasuwar Ƴan Jarida Sakamakon Hatsarin Mota
Anwarul qalam tare da haɗin guiwar Markazul Fajr a karon farko sun gayyato mata 100 a ƙarƙashin jagorancin Malam Ahmed Zailani Kobi da wata mata da ta bayar da tallafin abinci da abin sha ga mahalarta taron karawa juna sanin don karfafawa matan guiwar shiga irin wannan taron bitar.
Dr. Abdullahi Hannafi Abdurrahman da ke jami’ar Kasheri a jihar Gombe ya kasance mai gabatar da lacca tare da Farafesa Hamza Abubakar da Malam Khalid Ibrahim Idris sun ja hankalin mahalarta taron su zauna lafiya da mazajen su.
Haka kuma sun koyar da su hanyoyin sana’a da dogaro da kai a gidan aure don a samu ci gaba mai dorewa a duk lokacin da mata a gidan aure ke da abin yi.
Read also: Ƙungiyar PTA First Lady College Ta Yi Allah-Wadai Da Bikin ‘Candy’ Ta Buƙaci Ɗaukin Gwamnati
Zargin Almundahana: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Riƙe Kuɗin Kano Da Aka Karkatar
Cikin malaman da suka gabatar da lacca a wajen taron akwai Malama Khadija Abdullahi da Injiniya Maimuna Sani da Dr Hussaini D. Gambo da Khalid Ibrahim Idris da Murtala Sabo Baban Takko yadda kowane daga cikin su ya gabatar da jawabai kan hanyoyin da za su taimaki sabbin amare da wanda suke gidan aure sanin yadda za su zauna da mazajen su lafiya.



























