Gwamna Inuwa Yahaya Ya Kaɗu Matuƙa Da Rasuwar Ƴan Jarida Sakamakon Hatsarin Mota
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya samu mummunan labarin hatsarin da ya faru da ƴan jarida, ma’aikatan Hukumar Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) Gombe, da Ma’aikatan Yaɗa Labarai cikin tsananin baƙin ciki, firgici da juyayi.
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli ya sanar da haka ga manema labarai.
Zargin Almundahana: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Riƙe Kuɗin Kano Da Aka Karkatar
Hatsarin ya faru ne a kan hanyar Ɓilliri zuwa Kumo yayin da waɗanda abin ya shafa ke dawowa daga bikin auren abokiyar aikinsu a Kaltungo.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hatsarin a matsayin wani mummunan lamari mai tayar da hankali wanda ya jefa Jihar Gombe cikin jimami, yana mai cewa rashin ya wuce na iyalai da hukumomi, ya ma taɓa ruhin kafofin watsa labarai da ma’aikata baki ɗaya.
Waɗanda suka rasa rayukansu a cikin wannan mummunan lamari sun haɗa da: Zarah Umar, Manajar Labarai kuma Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Gwamna a Ofishin Uwargidansa; da Manu Haruna Kwami, Manajan Gudanarwa na NTA; da Isa Lawan; da Musa Tabra, Tsohon Manajan Labarai; da Aminu Adamu, Babban Direba; da Adams Ɗanladi na StarTimes; da kuma Judith Kutus, Jami’ar Yaɗa Labarai ta Hukumar Ilimin Bai Ɗaya Daga Tushe ta Jihar Gombe (SUBEB).
Read also: Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano
Gwamnan yace mamatan ƙwararru ne da suka sadaukar da rayuwarsu wajen faɗakarwa, ilmantarwa da kuma yi wa jama’a hidima, yana mai bayyana mutuwarsu a matsayin mummunan koma-baya ga aikin jarida, da ayyukan gwamnati da kuma shugabanci a Jihar Gombe.
“Wannan ibtila’in abin tausayi ne ƙwarai. Mun rasa abokan aiki, abokan hulɗa a fagen ci gaba, kuma ma’aikatan gwamnati masu himma waɗanda suka yi aiki tuƙuru da kuma jajircewa. Za mu daɗe muna jimamin wannan rashin a tsawon lokaci,” in ji Gwamnan.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, da shugabanni da membobin ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, da shugabanni da ma’aikatan hukumar talabijin ta Najeriya NTA da kuma dukkanin ‘yan jarida da ma’aikatan kafofin watsa labarai a ciki da wajen Jihar Gombe.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma nuna matuƙar damuwa ga waɗanda suka ji rauni, waɗanda a halin yanzu ake kula da su a asibiti, ciki har da Emmanuel Akila (Wakilin Gidan Talabijin na NTA a gidan Gwamnatin Gombe), da Steven Doddo na Sashin Tallace-tallace na NTA, da Nina Gadal ta Ma’aikatar Yaɗa labarai), da Jonathan Bara, Manajan Tallace-tallace na NTA. Gwamnan ya tabbatar musu da cikakken goyon bayan gwamnati.
“Zuƙatanmu suna tare da waɗanda suka ji rauni, kuma muna addu’ar Allah ya basu lafiya cikin sauri. Gwamnatin Jihar Gombe tana bin diddigin lamarin sosai kuma za ta tabbatar da cewa an samar da duk wani taimako da ake buƙata,” in ji shi.
“Wannan lokaci ne mai tsauri ga Jihar Gombe. Muna jimami da makoki tare, muna alhini tare, kuma muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya kare mu duka daga irin wannan mummunan lamari,” in ji Gwamnan.
Read also: Mutane 12 Sun Hallaka A Yayin Da Wasu Suka Jikkata A Haɗarin Mota A Kano
Duk Wanda Ya Tafi Jam’iyyar APC ya Tafi Shi Kaɗai, In ji Sanata Rufai Sani Hanga
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya jiƙan waɗanda suka rasu ya gafarta musu, sannan ya baiwa iyalansu, da abokan aiki da kuma masoyansu karfin jure wannan babban rashi.




























