Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Daga TSN Hausa
Ɗan jarida daga Jihar Kano ya bayyana shirin sa na kai ƙarar hadimin gwamnan Abba Kabir Yusuf a gaban kotu biyo bayan zargin cin mutuncin sa gami da yunƙurin dukansa a bainar jama’a a yayin gudanar da aikin sa.
Lamarin ya faru ne a lokacin atisayen tseran motoci a filin sukuwa da ke Kano a wani ɓangare na shirin bikin gasar kamun kifi da ake gudanarwa a garin Argungu dake Jihar Kebbi, na cikar bikin shekaru 61 da gudanar mashahuriyar al’adar.
Auwal Sani Rogo, SSR na Gwamna Jihar Kano, shi ake zargi da tozartar da ɗan jaridar Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai, wanda ke gudanar da aikin sa a wannan taro.
Aƙalla Ɗalibai Mata Dubu 12,133 Zasu Sami Tallafin Karatu Na AGILE A Bauchi
Shaidun gani da ido, sun bayyana cewa cin mutuncin ya faru ne bayan Sharifai da wasu ‘yan jarida sun yi hira da wasu ma halarta taro a gurin.
Read also: One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano
Lamarin ya faru ne a gaban manyan jami’an gwamnati ciki har da Ibrahim Abdullahi Waiya, kwamishinan yaɗa labarai da harkokin Cikin Gida da Hajiya Aisha Lawan Saji Rano, kwamishinar Harkokin Al’adu da Yawon Bude Ido da kuma Alhaji Abba El-Mustapha, shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano.
Bayan faruwar lamarin, Sharifai ya shigar da korafi a ofishin ‘yan sanda na Bompai, sai dai Rogo bai amsa kiran ‘yan sanda ba, yana amfani da girman kujerarsa gani yana aiki a Gidan Gwamnatin Jihar Kano a matsayin kariya daga kama shi.
Kwamishinan Waiya ya gayyaci ɗan jaridar domin tattaunawa, inda ya yi alkawarin shiga tsakani domin nema wa Rogo afuwa.
Sai dai har yanzu babu wani bayani ko neman afuwa daga Rogo ko gwamnatin Jihar Kano, ko ofishin mashawarci na musamman ga gwamnan Abba Kabir Yusuf.
Majiyoyi kusa da Sharifai sun ce idan har ba a dauki mataki ba, kotu ita zata zama raba gardama.
Lamarin yana ci gaba da jawo muhawara a tsakanin ‘yan jarida a Kano ganin yadda ake cin zarafin yan jarida duk da kariya da kundin tsarin mulki ya ba su.
Read also: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Kaɗu Matuƙa Da Rasuwar Ƴan Jarida Sakamakon Hatsarin Mota
Jaridar TSN ta yi ƙoƙarin samun wanda ake zargi domin jin ra’ayinsa game da zargin amma hakan ya ci tura, domin mun kira wayar sa bai dauka ba.



























