Mutane 12 Sun Hallaka A Yayin Da Wasu Suka Jikkata A Haɗarin Mota A Kano
Daga Sani Aminu
Read also: Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano
Mummunar Haɗarin mota ya yi sanadiyar rasuwar akalla mutum Sha biyu, yayin da wasu biyar suka jikkata, a kan titin hanyar Kano zuwa Zariya.
Haɗarin ya faru a safiyar Juma’a, da ta gabata a ƙauyen Samawa a ƙaramar hukumar Garun Malam dake Jihar Kano.
Read also: Ambaliya ruwa ta hallaka mutane sama da 100 a jihar Texas ta Amurka
Bayanan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano sun nuna cewa hatsarin ya auku ne misalin ƙarfe 2:40 na safe a kan titin Zaria zuwa Kano, inda babbar mota kirar DAF CF95 mai ɗauke da kaya da fasinjoji ta kauce daga kan hanya.
Mai magana da yawun FRSC a Kano, Abdullahi Labaran, ya bayyana cewa daga cikin mutum 19 da ke cikin motar, 12 sun mutu a wurin, biyar sun jikkata, yayin da biyu suka tsira ba tare da rauni ba.
- Amnesty ta zargi sojojin Najeriya da yin kisan gilla a yankin Kudu maso Gabas
- Yan Daba Sama Da 500 Sun Tuba Tare Da Ajiye Makamansu A Kano
- Tsofaffun Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Barranta Kansu Da Maganganun Shugaban APC Kano Abdullahi Abbas
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kura domin samun kulawa, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a dakin ajiye gawa na Asibitin Nassarawa.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Hukumar FRSC ta yi kira ga direbobi, musamman masu tukin dare, da su kiyaye ƙa’idojin tuki, tare da gujewa lodin kaya fiye da ƙima.
Rahotanni sun nuna cewa yawaitar irin waɗannan haɗurra a manyan titunan ƙasar na ƙara tayar da hankali, musamman waɗanda suka shafi manyan motoci masu ɗauke da kaya da fasinjoji.



























