Zamfarawa Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 37 A Kokarin Kwatar Kai
Al’ummar Ƙauyen Matusgi da ke Talatar Mafara a jihar Zamfara, Najeriya, sun fara kwatar kansu daga hannun ‘yan ta’adda, a inda sukai nasarar hallaka ‘yan bindigar 37 har lahira bayan sun farwa kauyen da nufin satar mutane don neman kudin fansa.
Read also: Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi
Kafar sadarwar, Alfijir Labarai ta rawaito lamarin ya faru ne bayan da mazauna kauyen suka yi artabu da ‘yan bindigar da suka mamaye ƙauyen da nufin yin garkuwa da mutanen gami da kwasar dukiyarsu.
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Mutanen garin sun lashi takobin kin amincewa da cin-kashin-kajin da ‘yan bindigar ke musu, na daka musu wawa domin neman kuɗin fansa da kuma wawashe abinci su dama ko wace irin kadara da sukai ido biyu da ita
A Karanta Wanna:Karamar Hukumar Ghari Ta Raba Takardun Daukar Aiki Ga Malamai 50
Zamfarawa sun ce ba zasu kara yarda a rinka cin su da basila ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, inda al’ummar ƙauyen suka yi dafifi dauke da makamai kada-kada inda Allah ya basu nasarar cimma ‘yan ta’addan bayan artabun da suka yi.
Read also: Motar Dangote Ta Kashe Mace Mai Ciki, Yaro Da Mutum Shida A Ondo
Idan za a tuna ƙauyukan Zamfara da makwabtanta suna nema su zama a hannun ‘yan bindiga ta hanyar kwashe mutane don neman kudin fansa da kakkaba musu harjin ba-gaira-ba-sabar kafin su noma gonakinsu gami da cin karansu babu ko babbaka ta aiwatar da ta’addanci kala-kala ba ko shaƙar hukuma.
A Karanta Wanna:Al’ummar Unguwar Tarauni Sun Koka Game Da Ambaliyar Ruwa Dake Barazanar Lakume Gidajensu




























