Ƙasurgumin Dan Dabar Da Ya Addabi Jama’a A Kano Burakita Ya Sheka Barzahu
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewar ƙasurgumin dan daban da ya addabi unguwar Dorayi da wasu unguwanni a jihar Kano Abba Burakita ya mutu.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da haka ta kafar sadarwasa ta Facebook.
A Karanta wanna:Rukakken Dandaba Burakita Ya Gamu Da Fushin Jama’a Yana Tsaka Da Kwaccen Waya A Kano
Read also: Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA
Inda ya ce Burakita yana daga cikin ‘Yan daban da suke nema ruwa a Jallo.
Jama’a sun kamashi tare da yi masa duka bayan ya fito shi da gunggun yaransa suna Kwaccen waya a Polo a karshe, ya mutu bayan da aka kai shi Asibitin Murtala likitoci suka tabbatar da cewa ya Mutu.” Inji Kiyawa.
Burakita ya dale yana aikata ta’addanci na fashi da makami da Kwaccen waya da makamantan su a jihar Kano.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
A Karanta wanna:Zamfarawa Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 37 A Kokarin Kwatar Kai
Idan za a tuna Burakita yana cikin yan sandan sarauniya da ya rungumi zaman lafiya a 2023 a bisa kokarin Kwamishina ‘yan sanda na wancan lokaci a Kano, amma abin takaici ya koma ruwa.




























