Rukakken Dandaba Burakita Ya Halu Da Fushin Jama’a Yana Tsaka Da Kwaccen Waya A Kano
Daga Wakilinmu
Read also: Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA
Al’umma a jihar Kano sun yi kukan kura sun dakume gawurtaccen ɗandaban nan mai suna Abba Burakita a titin zuwa gidan gwamnati yana kan sana’arsa ta kwaccen waya bayan ya zarewa mutum makami.
Kafor yada labarai ta STENTORNEWS ta rawaito tabbacin dakume wanna takadirin Dan-dabar bayan da ya fito shi da tawagarsa suna tsaka da kwacewa mata da matasa wayoyinsu na hannu da babaura da kuɗaɗe ko kuma duk wani abun amfani a jikin mutumin da tsautsayi ya fadawa.
A Karanta Wanna:Zamfarawa Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 37 A Kokarin Kwatar Kai
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da ake wasan Polo a yammacin Juma’ar nan a Unguwar Nasarawa.
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Majiyar ta ce mutane sun yi kukan kura ne inda su ka afkawa ‘yandabar kuma nan take suka kama babban nasu wato Abba Burakita, aka Kuma karairaya kafafuwansa da hannayensa baya ga raunuka ko ina a jikinsa.
A Karanta Wanna:‘Yar Shekara 35 ta Rasu, ‘ya’yenta Biyu Sun Jikkata Sanadiyar Faduwar Gini a Unguwar Makwarari A Kano
Daga bisani suka miƙa shi ga jami’en tsaro na ‘yan sanda a Kano domin gudanar da bincike.
Burakita na daga cikin kasungumin ‘yan dabar da suka addabi jihar ta Kano, wanda daga bisani ya miƙa kansa ga rundunar ‘Yan sanda, bayan hukumar ‘yan sanda ta ayyana nemansa ruwa a jallo.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
A Karanta Wanna:Akalla Mutane 20 Sun Hallaka Ya Yin Da Suke Tserewa Farmakin ‘Yan Bindiga a Zamfara
Ta’adar kwaccen waya ko ince fashi da makami ya zama ruwan dare a Kano da ma sauran jihohi na arewa, dukka da kokarin hukumomin tsaro amma abin yana nema ya gagari kundila. Me yiwa hakan ce tasa mutane suka fara fito-na-fito da irin wadannan takadarun matasa, Allah ya shirya su.
Alfiri Labarai




























