Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

‘Yar Shekara 35 ta Rasu, ‘ya’yenta Biyu Sun Jikkata Sanadiyar Faduwar Gini a Unguwar Makwarari A Kano

Gidan da ya rushe a Unguwar Makwarari
Gidan da ya rushe a Unguwar Makwarari

‘Yar Shekara 35 ta Rasu, ‘ya’yenta Biyu Sun Jikkata Sanadiyar Fadawar gini a Unguwar Makwarari A Kano.

Daga Wakilinmu

Sakamakon ruwan sama da aka tafka a ranar Alkhamis zuwa wayewar gari Juma’a da ta gabata yai sanadiyar rushewar gidan Ma’aikacin Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Kano Tijjani Magaji (Cameraman), wanda kuma wakiline a Ma’aikatar Matasa ta jiha wanda iftila’i yai sanadiyyar rasuwar matarsa.

‘Yar shekara 35, Balaraba Tijjani ta rasu a ranar Juma’a yai sanadiyyar rushewar gidan da suke zaune a unguwar Makwarari wanda hakan yai ajalinta a inda ‘ya’yenta biyu, Abdulnasir da Abdallah masu shekaru 11 da 13 suka samu raunuka.

Da yake zantawa da kafar yaɗa labarai ta STENTORNEWS, mijinta Tijjani Magaji ya ce gidan ya rushe sakamakon ruwan sama da aka samu mai yawa a daran Alkhamis zuwa wayewar gari Juma’a a inda basu yi aune ba sai jin faduwar gini sukai gaba ɗaya.

A Karanta wanna:Zamfarawa Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 37 A Kokarin Kwatar Kai

Ya ce mutanan unguwa ne suka zakulota daga cikin ƙasa tare da ‘ya’yenta guda biyu waɗanda nan take aka kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, amma daga bisani matar rai yai halinsa sakamakon tsinkewar da lakarta ta yi, bayan da likitoci suka tabbatar da hakan. Haka kuma yaran suka samu raunuka.

Malam Magaji ya danganta iftila’i daga hukuncin Allah Maɗaukakin Sarki tare da yi mata addu’a da sauran waɗanda suka gabata domin samun gafara Allah (SWA). Ya kuma gode wa jama’ar unguwar bisa agajin gaggawa da suka basu.

Cikin yanayi na tausayi, Malam Tijjani, ya roki Gwamna Jiha Alh. Abba Kabir Yusuf da ya kawo musu ɗauki domin samun damar gyara mutsiguni duba da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa kamar yadda ya zanta da wakilinmu idonsa na zubar da hawaye.

A Karanta Wanna:Al’ummar Unguwar Tarauni Sun Koka Game Da Ambaliyar Ruwa Dake Barazanar Lakume Gidajensu

Tuni masana yanayi na kasa (NEMA), su kai hasashen samun ruwan sama mai yawa a bana tare da samun ambaliyar ruwa musamman a jihohin Arewa ciki har da jihar Kano, wanda hakan yake haifar da rushewar gidaje da shafewar gonaki da koguna da kuma karyewar gadoji a wasu sassa daban-daban.

← Back

Thank you for your response. ✨

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...