Mutane 16 Gini Ya Faɗawa A Unguwar Dandishe A Kano
Daga Wakilin mu
KANO– Akalla mutane 16 ne gini ya rufta a kansu a yankin Dandishe, Kwanar Yashi, da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano Najeriya.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi, Mutane na Sambarka
Rahotanni sun ce jami’an ceto sun samu nasarar fitar da mutane 13 daga cikin ginin da ransu, ciki har da yara shida.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ginin ya rufta da misalin ƙarfe 4:32 na asubahin ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce jami’an ceto sun garzaya wurin bayan samun kiran neman agaji.
Bayan isarsu wurin, jami’an sun gano cewa wani gini mai girman kusan ƙafa 20 da 30 ya rufta, lamarin da ya rutsa da mutane 16.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA
Hukumar ta ce an yi nasarar ceto mutane 13 da ransu, ciki har da yara shida, a inda ragowar guda uku aka garzaya da su Asibiti saboda suna cikin matsanancin yanayi domin samun kulawar likita.
Haka kuma babu cikakken bayanin musabbabin ruftawar ginin, amma ana ci gaba da bincike domin.
Read also: Mutane 12 Sun Hallaka A Yayin Da Wasu Suka Jikkata A Haɗarin Mota A Kano
Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ko akwai wasu mutane da suka rasa rayukansu ko suka samu raunuka sakamakon lamarin ba.




























Pingback: Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha - The StentorNews Hausa