Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA
Daga Wakilinmu
Sakamakon saɓawa dokokin tsare-tsaren gine-gine da kin bin umarn, Gwamnatin Kano ta bada umarnin rushe wani dogon gini da ake ginawa a Nassarawa GRA
Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Gine-Gine ta Jihar Kano (MLPP) ta rushe ginin a unguwar Nassarawa GRA, kusa da titin AVM Mukhtari Muhammad, bayan an tabbatar da cewa ya saɓa wa dukkanin ƙa’idodin tsare-tsaren gine-gine da aka amince da su a jihar.
Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi, Mutane na Sambarka
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
A cewar Ma’aikatar, wanda ke gudanar da aikin ginin ya yi watsi da umarnin hukuma na dakatar da aikin duk da gargaɗin da aka yi masa sau da dama, lamarin da ya sa gwamnati ta ɗauki matakin tabbatar da bin doka.
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta kare babban tsarin bunƙasa birane na jihar (Master Plan), tare da gargaɗin cewa duk wani gini da ya saɓawa ƙa’ida zai fuskanci irin wannan mataki domin tabbatar da an bi doka da oda.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi, Mutane na Sambarka
Idan za a tuna a satin nan Shugaban Kwamitin kar-ta-kwana mai binciko gine-gine da aka yi su ba bisa ka’ida ba, Dr Dalhatu Aliyu Sani, ya ce daga kafa kwamitin sun binciko gurare da akai gine-gine sama da 300.



























