Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Ƙirƙirar Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Ya Saɓawa Doka, In Ji Farfesa Mai Bushira

Hisbah
Hisbah

Ƙirƙirar Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Ya Saɓawa Doka, In Ji Farfesa Mai Bushira

Daga Sunusi K/Naisa

Shugaban Kwamitin masu ruwa da tsaki na Hisbah, Farfesa Ibrahim Mu’azzam Mai Bushira, ya yi gargaɗi kan yunƙurin kafa wata hukumar Hisbah mai zaman kanta a Jihar Kano, yana mai cewa ba ya doron doka, kuma zai iya haifar da ɓaraka da taɓarbarewar zaman lafiya da kuma matsaloli ga tsarin tsaro a jihar.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kano ranar Alhamis, Farfesa Mai Bushira ya ce kwamitin ya cimma wannan matsaya ne daga taron masu ruwa da tsaki, wanda ya ƙunshi tsofaffin shugabannin Hisbah da Mataimakan su da duk manyan Sakatarori da suka gabata. Ya ce taron ya yi duba na tsanaki tare da tanttance illolin kafa wata sabuwar Hisbah a lokacin da jihar take da hukumar Hisbah guda ɗaya da doka ta amince da ita, wacce Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa.

Ya ce lamarin samar da sabuwar Hisbah wanda ake dangantawa daga tsohon Gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai janyo rarrabuwar kai da rikice-rikice a cikin jihar ba tare da kawo wani amfani ba.

Gwamnatin Kano ta Nemi Jami’an Tsaro Su Kama tsohon Gwamna Ganduje da Barau Bisa Zargin Kalaman Tunziri

“Mun fahimci cewa wannan lamarin ya taso ne sakamakon korar wasu jami’an Hisbah da Marshals da akai. Amma a matsayinsu na Musulmai kuma masu ruwa da tsaki a Kano, mun san cewa wannan ba ya cikin muradin kowa,” in ji shi.

Farfesa Ibrahim Mai Bushira ya yi gargaɗin cewa kafa wata Hisbah dabam wadda ke da irin ayyukan hukumar a dokance “zai kawo matsaloli da dama, ciki har da waɗanda muka hango da waɗanda ba mu iya hasashe ba.” Ya ce maimaita irin wannan muhimmin aiki na iya janyo rikice-rikicen aiki da kuma raunana tsarin tsaro da ke aiki a yanzu.

Ya tuna cewa lokacin da ake tsara dokar kafa hukumar Hisbah ta yanzu, dukkan waɗanda suke cikin ƙungiyoyin Hisbah masu zaman kansu a wancan lokaci an haɗa su cikin tsarin hukumar Hisbah domin gujewa rarrabuwar kai da tabbatar da haɗin kai.

Shugaban ya nanata cewa dole a ci gaba da kare ƙa’idojin  haɗin kai da bin doka, da tsare-tsaren tsaro na bai ɗaya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano mai ɗorewa.

Da yake bayyana mana ra’ayinsa, wani ɗan asalin jihar Kano, ya ce yunƙurin kafa wata sabuwar Hisbah ta daban ka iya haifar da matsin lamba ga Gwamnatin Tarayya domin ta haramta Hisbah a Kano da ma Arewa baki ɗaya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...