Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya

Gunmen
Gunmen

Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya

Daga Wakilinmu 

Wani bincike na SBM Intelligence ya binciko cewa hare-haren garkuwa da mutane sun ƙaru da kashi 66 daga cikin ɗari idan aka kwatanta da zangon da ya gabata na shekarar 2025.

Rahoton bincike na SBM Intelligence ya ce an sace mutane 7,825,1713 a Najeriya tsakanin watan Yuli 2025 zuwa Yuni 2026, yayin da mutane 1,142 suka rasa rayukansu.

Rahoton mai taken ‘The Capture of the
Kidnap Economy’ a turance, ya ce an biya jimillar sama da naira biliyan 7.8 a matsayin kudin fansa. A inda ya ce kaso 90% na kuɗin fansar da aka biya sun tafi ne ga ɓangaren JAS na Boko Haram daga cikin hare-hare takwas.

Sojoji Sun Dakile Harin Lakurawa, Sun Kwato Makamai da Ceto Dabbobi 62

SBM Intelligence ta ce hare-haren garkuwa da mutane sun ƙaru da kashi 66% idan aka kwatanta da zangon da ya gabata, rahoton ya nunar jihohin Arewa maso Yamma ne suka fi fuskantar hare-haren a wannan shekara. A inda Zamfara ta samu hare-haren 2,362 wanda ya yi sanadiyyar sace mutane 1,921.

Rahoton ya ce sace mutane da yawa lokaci guda shi ne hanyar da masu garkuwa suka fi amfani da ita, yayin da a wasu lokuta aka kashe waɗanda aka yi garkuwa da su duk da an biya fansar.

AN YI KARE JINI BIRI JINI DA YAN BINDIGAR DA SUKA TARWATSA WASU YANKUNAN ALKALERI A BAUCHI

SBM Intelligence sun ba da shawarar ga gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaro da su duƙufa wajen ganowa gami da daƙile hanyoyin samun kuɗaɗen da ke tallafa wa ayyukan ta’addanci da kuma magance matsalolin tattalin arziki da ke ƙarfafa wannan laifi.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Sarkin Noma Nadabo Chiromawa Ya Kubuta, Yana tare da Iyalan Sa - The StentorNews Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...