Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Gami Da Garkuwa Da Wasu A Kano

'Yanbindiga
'Yanbindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Gami Da Garkuwa Da Wasu A Kano
Daga Edita

Akalla mutane uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu uku suka fada hannun ‘yan bindiga a wani sabon hari da aka kai a kananan hukumomin Shanono da Tsanyawa a Jihar Kano.

Majiyoyi daga yankin sun ce, ‘yan bindigar ɗauke da makamai masu yawa sun shigo jihar ta iyakar Katsina, inda suka fara kai hari a garuruwan Yanganau da Tsanyawa tun yammacin ranar Alhamis.

Bincike ya nuna cewa, jami’an tsaro sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, inda suka fatattake su daga wurin harin farko. Babu wanda aka jiwa rauni, sai dai an sace wasu dabbobi.

Wani mazaunin yankin ya bayyana wa majiyarmu cewa, “Sun fito ne daga Kogari, Musawa/Matazu, na Jihar Katsina. Jami’an tsaro sun samu labari misalin karfe 5:30 na yamma, amma bayan musayar wuta, ‘yan bindigar suka tsere.”

A Tsanyawa kuwa, ‘yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare a Yar Tsamiya, da Faruruwa da Shanono misalin karfe 1:30 na dare.

A nan ne suka kashe mutane uku sannan suka yi garkuwa da wasu uku kafin su tsere.

Farfesa Muhammad Dauda daga Kuraku ya ce, “A cikin kwanaki uku, hare-hare sun shafi unguwanni Tsamiya, Yaudari da Yanganau. Mutane sun mutu, wasu kuma sun bace. Mutanenmu suna kwana a daji ko wurin ‘yan uwa saboda tsoro.”

Har zuwa yanzu, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma ba.
Izuwa yanzu mun sami majiyarmu ta ce Jami’an tsaro sun Kama mutane biyu da suke kai wa ‘Yan Bindiga Kayan masarufi.
Inda Ranka

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...