Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Ziyarartar Makarantun Kwana

Gov Abba Kabir Yusuf
Gov Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Ziyarartar Makarantun Kwana
Daga Sunusi K/Na’isa

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, a matsayin ranar kai ziyara ga dukkan makarantun gwamnati na kwana na firamare da sakandare a fadin jihar.

A cewar sanarwar da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Musbahu Aminu Yakasai, ya sanya wa hannu tare rabawa manema labarai, sanarwar ta bukaci iyaye da masu kula da yara su kai ziyara ga ‘ya’yansu daga karfe 9:00 na safe zuwa 5:00 na yamma.

Sanarwar ta ruwaito Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya bayyana godiyarsa ga iyaye da masu kula da yara, da sauran masu ruwa da tsaki a fanin ilimi bisa goyon baya da haɗin kai da suke ba ma’aikatar sa. Haka kuma ya yi fatan samun nasara a yayin gudanar da ziyarar a dukkan makarantun kwana na jihar.

Ga Wani Labarin:Gwamna Kano Abba Ya Amince da Rushe Hukumar Kula da Kare Haƙƙin Mai Saye Da Mai Sayarwa Ta Kano Nan Take

“Ma’aikatar ilimi na yabawa da haɗin kai da fahimtar da iyaye da masu kula da yara ke nunawa, wanda hakan ke ƙara ƙarfafawa ƙoƙarinmu na inganta harkar ilimi a Jihar Kano,” in ji Dr. Makoda.

Ya ƙara jaddada muhimmancin bin ƙa’idoji da dokokin da suka shafi ziyarar makarantu, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsari da tsaro da jin daɗin ɗalibai da masu ziyara yayin gudanar da ziyarar.

Ga Wani Labarin:Da Dumi-Dumi: Duk Wanda Aka Kama Da Lalata Yara Ƙanana Zai Fuskanci Hukuncin Daurin Rai-da-Rai, In ji Majalisar Dattawa

Ma’aikatar ta kuma tabbatar da aniyar ta na ci gaba da kare lafiyar dalibai tare da samar da yanayi mai kyau na koyon karatu a dukkan makarantun jihar, tare da kira ga iyaye su yi amfani da damar ziyarar wajen yin tattaunawa mai amfani da malamai da shugabannin makarantu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...