KSCHMA
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: BUDADDIYAR WASIKA GA GWAMNA KANO ABBA K. YUSUF !!!
A Yaɗa Labarin
Hukumar kula da Tsarin Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) ta lura da wasu bayanai da suke zagayawa a zaurukan sada zumunta, wadanda suke cike da kurakurai game da yadda tsarin hukumar yake tafiya. Tare da dukkan girmamawa ga masu yada irin wadannan zantuttuka, shi wannan tsari na taimakekeniyar kula da lafiya yana aiki ne a karkashin doka mai lamba uku ta shekarar 2016. Ana gudanar da shi ne a gwadaben abinda ake kira “Atta’awun” a addinin Musulunci, wato mai karfi ya taimakawa mai rauni domin a gudu tare a tsira tare.
Duk wani ma’aikaci da yake aiki a Jihar Kano, kama daga ma’aikatan gwamnati zuwa masu rike da mukaman siyasa (zababbu da nadaddu), ana yankar kudin taimakekeniyar kula da lafiya daga albashinsa dai-dai da girmansa a aiki. Duk ma’aikacin da yake kan wannan tsari yana da damar yiwa kansa rajista, da matarsa ta aure guda daya, tare da yayansa guda hudu. Wannan zai kama mutum 6 kenan. Kowanne wata KSCHMA tana tura naira 400 sau shida kenan zuwa ga asibitin da iyalin ma’aikacin sukai rejista, wanda zai kama naira 2,400 kenan. Kasancewar wannan tsari na taimakekeniya ne, da ma’aikacin da ake cirewa N4,000 da wanda ake cire masa N1,400 dukansu suna da damar saka matarsu guda daya da yara guda hudu ‘yan kasa da shekara 18. Kaga idan aka biyawa kowanne daga cikinsu da iyalansu N400 a wata kowa an biya masa N2,400, saboda haka wanda ya bayar da naira 1,400 abinda ake biya masa yafi karfin abinda yake bayarwa.
Read also: Kwamishina Lafiya Ya Magantu, Yadda Suka Sami Kasuwancin Magunguna A Kano
Ha Wasu Labaran:
- Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Al’ummar Gari A Garko Har An Kone Motar ‘Yan Sanda
- Gwamnatin Kano ta Sanar da Ranar konawa Makaranta
- Haramtacciyar Harkar Ma’adanai Ke Rura Wutar Ta’addanci A Najeriya, Kuma Wasu Manyan Mutane Ke Gudanarwa
Wannan kudin ne asibitocin suke amfani da su domin kula da lafiyar ma’aikatan da iyalensu a matakin farko (primary healthcare services). Ma’aikaci da iyalinsa zasu je asibitin da sukai rijista da shi domin kulawa da lafiyarsu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, kuma abinda za a nema su bayar kawai kaso 10 ne cikin dari (10%) na kudin magani da aka rubuta musu kacal. Misali, idan maganin 10,000 aka bawa ma’aikaci, to zai biya 1,000. Idan kuma an gamu da larura wacce take babba da take bukatar kulawa ta musamman (secondary healthcare services), asibiti zasu sanar da wannan hukuma nan take domin basu damar bayar da kulawa ta mataki na biyu ga mara lafiya. Bayan an gama, hukuma zata biyasu gabaki dayan abinda aka kashe ba tare da mara lafiya ya bayar da ko sisi ba.
Asibitocin da KSCHMA take aiki da su ana tura musu kudaden kula da lafiyar duk wanda yayi rajista ya kuma zabe su duk wata. Babu wani wata da aka taba tsallakewa ba a biya wannan kudade ba. Zasu sayi magani ne da kashi 70 cikin 100 na kudin da aka tura musu, kashi 30 cikin 100 kuma za suyi wasu ayyuka da hidimomi da suka shafi asibiti. Duk sanda mutum yaje asibiti ya tarar babu magani, akwai lambobin wannan hukuma a bangwayen wadannan asibitoci. Mutum zai iya kiran wadannan lambobin waya ya shigar da korafi kuma za a bi masa hakkinsa a tabbatar da cewa an bashi magani. Baya ga wannan dama, mutum ma zai iya zuwa wannan hukuma kafa da kafa domin shigar da korafi.
Kudaden Ma’aikata da ake turowa wannan hukuma suna zuwa ne duk wata kuma ana tura su zuwa asibitoci ba wai zama sukeyi a wannan hukuma ba. Wannan hukuma tana aiki kafada da kafada da duk masu ruwa da tsaki, ciki har da kungiyar kwadago ta jihar Kano, domin tabbatar da samar da ingantacciyar kulawa ga dukkan wanda sukayi rajista.
Read also: Gwamnatin Kano Na Faɗakar Wa Kan Cutar Lassa, Ta Ja Hankali Game Da Haɗarin Yaɗuwar Cutar
Tuntuɓe mu a:
27a Sokoto Road, Kano
Lambar waya: 09099990696 / 07044444926 / 08100637313
Shafin yanar gizo: kschma.org
Don yin rajista kai tsaye: mykschma.org
Sa hannu:
Aminu Ahmad Turaki
Jami’in Hulɗa da Jama’a na
Hukumar KSCHMA




























