Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Al’ummar Gari A Garko Har An Kone Motar ‘Yan Sanda

Konaniyar Motar Yan sanda
Konaniyar Motar Yan sanda

Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Al’ummar Gari A Garko Har An Kone Motar ‘Yan Sanda

Daga Edita

An kone motar ‘yan sanda a caji ofis ɗin rundunar ƴan sanda ta kasa reshen ƙaramar hukumar Garko dake Jihar Kano sakamakon arangama tsakanin Jami’an tsaron da al’ummar gari.

Global Trucker ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne sakamakon dagewa da masu haya da babura (‘yan Acaba) da sauran al’ummar gari su ka yi na dole sai an fito musu da wasu da ake zargin barayin babur ne sun kashe su.

Wasu Labaran:

Wani mazaunin garin da bai so a bayyana sunansa ba ya shaidawa majiyar mu cewa an kama mutanen da ake zargi sun kashe Ɗan acaban, bayan da suka sassara shi gami da yin awan gaba da babur dinsa kirar ‘Bajaj’ ta hanyar bibiyar wayar wanda aka kashe.

“Su wannan mutane ana zarginsu da tare wani Umar Idris Ɗan ƙauyen Kamfa a ƙaramar hukumar ta Garko, suka kwace masa babur kafin kazo tashar ilalu bayan ya dawo daga garin Buda, suka kuma kashe shi ranar larabar da ta gabata, to bayan an bibiyi wayarsa aka kama mutane biyu da ake zargi ciki harda Ɗan uwan Marigayin, bayan an kama su ne abokan sana’ar Marigayin da sauran al’umma suka dage dole sai an fito musu da waɗanda ake zargi suma su kashe su, lamarin da ya janyo fito-na-fito tsakanin ‘yan sanda da Al’ummar Gari,” inji Majiyar GLOBAL TRACKER.

Wata majiyar ta tabbatar mana da an kone motar, Amma baza ta iya tantance ko motar ‘yan sanda ba ce ko kuma wasu daga cikin motocin da aka ajiye a ofis ɗin ba ne.

Sai dai a dai-dai lokacin haɗa wannan rahoto mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce yana cigaba da binciken lamarin domin samun haƙiƙanin abin da ya faru.
Historical

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...