Tsaro: Hukumar Yan sanda ta Haramta Yin Wasan Tashe
Daga Sunusi K /Naisa
Read also: Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Al’ummar Gari A Garko Har An Kone Motar ‘Yan Sanda
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta sanar da dakatar da wasan Tashe a wannan watan na Ramadan, tana mai danganta matakin da matsalolin tsaro.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a, Abdullahi Kiyawa, ya fitar, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne tare da hadin gwiwar gwamnatin jiha domin hana ɓata-gari amfani da taron wajen aikata laifuka.
Sanarwar ta bayyana cewa an lura da yadda wasu ke amfani da lokutan Tashe wajen faɗan daba da sata da kwace waya da shaye-shaye gami da aikata miyagun laifuka daban-daban.
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Kwamishinan “yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bukaci iyaye da masu kula da yara su gargadi ‘ya’yansu da su guji duk wani abu da zai tayar da tarzoma a lokacin azumi.
AN YI KARE JINI BIRI JINI DA YAN BINDIGAR DA SUKA TARWATSA WASU YANKUNAN ALKALERI A BAUCHI
Rundunar ta yi wa al’ummar Kano fatan samun zaman lafiya tare da jaddada cewa duk wanda aka kama da karya doka zai fuskanci hukunci.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Kamar yadda aka sani Tashe dai al’ada ce mai tsohon tarihi a ƙasar Hausa da ake yi tun daga 10 farko na dararen watan Ramadan, wadda ta yaɗa da wasannin kwaikwayo, kaɗe-kaɗe da wasanni barkwanci. Amma a haɗin yanzu matasa sun mai da lokacin ya zama na tayar da hankalin al’umma tamkar a filin Gaza.



























