Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

Makarantar Zam-Zam International ta Yaye Ɗalibai 28 Mahaddata Al-Qur’ani, Ciki Har da Asiya Usman

IMG 20250208 WA0006
IMG 20250208 WA0006

Makarantar Zam-Zam International ta Yaye Ɗalibai 28 Mahaddata Al-Qur’ani, Ciki Har da Asiya Usman

Makarantar Zam-Zam International ta yaye ɗalibai ashirin da takwas mahaddata Al-Qur’ani Mai girma a karo na farko tun bayan kafuwarta. An gudanar da taron ne a ranar Asabar a harabar makarantar da ke Hotoro Kudu da ke kan titinTsamiyar Boka a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano a Najeriya.

IMG 20250208 WA0006

Taron mai kayatarwa ya samu halartar malaman addinin musulunci da Sarakuna gargajiya da ’yan siyasa da masu hannu da shuni.

Shugaban yayi alkawarin bada tallafin Ƙaramar Hukumar don haɓaka karatun Alqur’ani da sauran ilimi a duk lokacin da ake bukata.

A Iya Karanta Wanna:DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2)

Tun da farko, ɗaya daga cikin iyayen makarantar, Farfesa Sunusi Yuguda, ya bayyana nasarorin da makarantar ta samu, ciki har da samun dawamamen mutsuguni da kuma karuwar yawan ɗalibai, wanda ya ce a halin yanzu sun haura 3000. Ya taya mahadatan murna kuma ya ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da neman ilimin Alƙur’ani da bincike akan sauran ilimi da kuma yaɗa ilimin addinin Musulunci.

A Iya Karanta Wanna:Wani Sanata A Nijeriya Ya ce Sun San Manyan Hafsoshin Sojan Da Suke Hakar Ma’adanai Babu Izini

Farfesa Yuguda, ya kuma yi kira ga gwamnatocin jiha da ta ƙaramar hukumar Nassarawa da su tallafa wa makarantar ta hanyar samar da karin ajujuwa da malamai saboda karuwar yawan ɗaliban makarantar.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Taura, Hon. Shu’aibu Hambali Zangi, ya sanar da bayar da gudummawar Naira Dubu Dari Biyar (₦500,000) don tallafawa ɗalibai waɗanda iyayensu ba za su iya biyan kuɗin makaranta ba. Har ila yau, ya yaba wa malamai, ɗalibai, da iyaye saboda jajircewarsu wajen tabbatar da ‘yayensu sun sami haddar Alƙur’ani, tare da kira su ci gaba da neman ilimi.

Alhaji Idris Bello (Kawu), uba ga ɗaya daga cikin mahaddata Al-Qur’ani, Asiya Usman Bello, ya jaddada cewa sadaukarwar iyaye da juriya gami da addu’a na daga cikin muhimman matakai wajen samun nasarar ilimin yara. Ya bayyana mahaifin Asiya a matsayin mahaifi mai jajircewa da kulawa, kuma ya karfafa wa sauran iyaye da su ba da muhimmanci ga ilimin ‘ya’yansu.

IMG 20250208 WA0008

Haka Malam Kawu, ya kuma yi addu’a don samun albarkar Allah ga ɗaliban gami da gode wa hukumomin makarantar.

Ka Iya Karanta Wanna:Daukewar Wutar Lantarki ta ‘Yan Dakikoki ta Jawo Biyan Diyar Sama Da Naira Miliyan 375

Malam Usman Bello, mahaifin Asiya, ya nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki da ya albarkace shi da samun mahaddaciyar Al-Qur’ani Mai Tsarki a cikin zuriyar sa tare da addu’ar samun jagoranci Allah a dukkanin rayuwar su.

Usman Bello, wanda kuma shi ne Babban Editan jaridar yanar gizo ta StentorNews, ya gode wa shugabancin makarantar da iyalai da abokai, da ‘yan jaridu da masu fatan alheri bisa goyon baya da addu’o’i wajen samun nasarar taron.

A madadin StentorNews online Jarida, dake ƙarƙashin kamfanin Stentor Communication & General Enterprises, tana taya Malam Usman Bello da Hafiza Asiya Usman Bello da iyalansu, da dukkan ɗaliban da suka kammala haddar Al-Qur’ani murna bisa samun wanna gaggarumar nasarar mai girma a rayuwa. Haka kuma muna addu’ar Allah ya ci gaba da ba su jagoranci da albarka ya kuma bawa kasarmu da wannan zaman lafiya da ƙaruwar arziki.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...