Wani Sanata A Nijeriya Ya ce Sun San Manyan Hafsoshin Sojan Da Suke Hakar Ma’adanai Babu Izini
Daga Wakilinmu
Sanata mai wakiltar jihar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce manyan hafsoshin sojan kasar nan da suka yi ritaya ne ke da hannu a ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kasar nan, kuma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu labarin munanan ayyukan su.
Mista Oshiomhole ya yi wannan zargin ne a ranar Juma’a a gaban kwamitin majalisar dattijai kan kasafin kudi lokacin da shugaban kwamitin majalisar dattawa kan bunkasa ma’adanai, Sanata Sampson Ekong, ya mika rahoton kasafin kudin shekarar 2025.
“Hakar ma’adinan da ake ci gaba da yi ba bisa ka’ida ba a fadin kasar nan, Janar-Janar din da suka yi ritaya ne ke aiwatar da su, kuma mun san su. Eh, mun san su. Babu wani a Afirka da bai san su ba, ”in ji Mista Oshiomhole, ko da yake bai ambaci sunaye ba.
Mista Oshiomhole, wanda ya rike mukamin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tsakanin 2018 zuwa 2019, ya ce a lokacin ne ya sanar da Buhari lokacin da ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suka hana mambobin jam’iyyarsa gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar a jihar Zamfara.
Read also: Sarakunan Jama’are Da Ningi Na Miƙa Ta’aziya Bisa Rasuwar Durbin Kano
Ka Iya Karanta Wanna:Kwamishina Lafiya Ya Magantu, Yadda Suka Sami Kasuwancin Magunguna A Kano
“Na yi wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika kan lamarin a lokacin da yake mulki,” in ji Mista Oshiomhole. “Wannan ya faru ne saboda wata tawagar da na aika domin ta je gudanar da zaben fidda gwani a wani wuri ta kawo min rahoton kalubalen gudanar da zaben fidda gwani a Zamfara saboda masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.”
Ya kara da cewa, “Idan har za a yi yaki da wannan barazana, akwai bukatar mu tura Sojoji, har ma da kashe duk wanda ke da hannu wajen hako mu’adanai ba bisa ka’ida ba. Ya kuma kamata mu tura JTF, wadanda suka hada da Sojoji, ‘Yan Sanda, Sojin Sama, domin yakar su.”
Ikirarin na Mista Oshiomhole ya ba da haske kan ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a wasu jihohin Arewacin Najeriya da kuma karuwar ‘yan fashi da makami a yankin.
Read also: An Caka wa Malamin Addini Wuka a Sakkwato, Masu Ibada Sun Kashe Wanda Ake Zargi
Ka Iya Karanta Wanna:DABARUN KIWON KAJI A LOKACIN YANAYIN SANYI (1)
A ‘yan shekarun nan, jihar Zamfara mai arzikin zinari, ta kasance cibiyar ‘yan fashi da makami, wanda masana da dama ke alakanta da ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar.




























